Mashahuran gine-ginen tarihi biyar da ke Afirka

Mashahuran gine-ginen tarihi biyar da ke Afirka

Masana kan ce duk al’ummar da ta bari tarihinta ya gushe to ita ma akwai yiwuwar gushewarta baki daya wata rana.

Kuma al’ummu da kasashe da dama na tinkaho da ababen tarihinsu, walau na mutanen da suka yi wasu ayyukan bajinta, ko na gine-gine ko na sauran al’amura.

Kasashe nahiyar Afirka na daga cikin da dama a duniya da aka san su da kayayyaki da wurare na tarihi daban-daban.

A nahiyar ne ma ake adane da gawar Fir’auna, wanda ya yi zamani da Annabi Musa tun dubban shekaru da suka gabata.

Wadannan wuraren tarihi na daga cikin abubuwan da ke jan hankalin masu yawon bude ido daga sassan duniya dabam-dabam, kuma suna taimaka wa kasashen wajen samun kudaden shiga masu kauri.

A wannan makalar, za mu duba wasu muhimman wuraren tarihi ne na Afirka da suka yi shuhura.

Babban Masallacin Djenne (Mali)

Wannan masallacin alama ce ta garin Djenne, wanda ya taba zama babbar cibiyar kasuwanci a tsakanin shekarar 800 zuwa 1250 Miladiyya.

An bayyana masallacin a matsayin gini mafi girma da aka gina a ban kasa, kuma yana da mulmulallun bangwaye, da aka gina da bululluka na kasa da yashi da duwatsu, sannan kuma aka yabe shi.

An fara gina shi ne a karni na 13, amma ginin na yanzu an yi shi ne a shekarar 1907.

Tsayin masallacin ya kai mita 16, kuma yana da hasumaya uku.

Ginin wannan masallaci dai yana kama da ginin kasa na gargajiya da aka sani a yankin arewacin Najeriya.

Duk shekara a cikin watan Afrilu ana sabunta ginin Babban Masallacin Djenne da yaben kasa a wani taron gayya da ake kira Crépissage.

Ana yin hakan ne don kare masallacin daga rushewa a yayin lokacin damina inda a kan shafe wata biyu ana mamakon ruwan sama a kasar.

Dalar Meroe (firamid) a Sudan

Wadannan daloli da ke da matattakala, an samar da su shekaru 300 kafin Miladiyya, kuma suna nan a yankin Nubia, waje mai nisan kilomita 200 daga Khartoum, babban birnin Sudan.

Wannan waje da ke karkashin hukumar raya ilimi da tarihi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ya taba zama hedikwatar daular Kushite, kuma ayyukan hakar kayan tarihi da aka yi sun gano fadoji da wuraren ibada da wajen wankan sarakai.

An samar da dalar ne da bulullukan kasar dutse, kuma suna da mataimaka a cikinsu.

Duk da cewa akwai fiye da daloli 250 a wannan yanki na Sudan da har suka fi na Masar yawa, amma da wuya a ga masu yawon bude ido a wajen.

Sai dai ba kamar na Masar ba, dalolin Sudan kanana ne.

Yankin da dalolin suke na wajen hamadar sahara ne mai tsananin rana da zafi.

El Jem (Tunisiya)

El Jem na daya daga cikin gine-ginen Rumawa da aka yi a Afirka. Wajen taron da ke Tunisiya ya zama na biyu mafi girma a duniya bayan wanda yake Rum.

An gina wajen ba tare da tushe ba, an samar da shi gaba daya da duwatsu, kuma har yanzu yana nan a tsaye daram, har ma da tagoginsa da kofofi da wuraren zama.

An yi imani da cewa an samar da wajen taron shekara 230 na Miladiyya, kuma sarkin wannan lokacin Gordian ne ya gina shi.

Ganuwar Birnin Kano (Najeriya)

An gina Ganuwar Birnin Kano don kare mazaunan tsohon birnin daga hare-haren wasu garuruwan.

An fara aikin gina ganuwar mai tsayin kilomita 14 a tsakanin shekarun 1095 da 1134, daga baya aka kammala ta a karni na 14.

A 1902 an bayyana Ganuwar Kano a matsayin “Kayan tarihi mafi shuhura a Yammacin Afirka”.

Akwai kofofin shiga gari 15 a jikin ganuwar daga dukkan bangarorinta.

Kofofin su ne; Kofar Mata da Kofar Wambai da Kofar Dawanau da Sabuwar Kofa da Kofar Mazugal da Kofar Na’isa da Kofar Nasarawa da Kofar Dan Agundi da Kofar Gadon Kaya da Kofar Famfo da Kofar Ruwa da Kofar Kabuga da Kofar Duka-wuya da Kofar Kofar Kansakali.

A yanzu ganuwar na fuskantar kalubalen sassake ta da mutane ke yi suna amfani da kasar wajen yin gine-gine.

Dalolin Masar

An gina su a zamanin da aka assasa sakafa mafi arziki da karfi a duniya, musamman ma manyan dalolin da ke Giza, sun zama daya daga gine-gine mafiya ban mamaki da aka samar a ban kasa.

Yanayi da zubinsu na bayyana irin rawar da fir’auna ko sarki ke takawa a tsakanin al’ummar Misirawa na wancan lokacin.

Bayan shekara dubu 4,000, har yanzu dalolin na Masar na nan a tsaye kyam da su.

Kuma suna daga cikin abubuwan ban sha’awa da ke jan hankalin masu zuwa yawon bude kasar, lamarin da ke samar wa Masar dumbin kudaden shiga.

TRT Afrika da abokan hulda