Daga Dayo Yussuf
Ciwon daji na jarraba mutane ta hanyar da babu wanda tsammata. Ana kira ga karfin gwiwa, imani, hakuri da juriya da tausasawa a lokacin da jikin dan adam ke fafutuka, zuciya kuma na kadawa.
Kevin Mwachiro dan kasar Kenya ya yi fama da duk wadannan da ma wasu, "Idan wannan Oktoban ya zo shekara tara kenan," in ji shi, bayan da aka gano yana dauke da cutar.
Ya wayi gari a Nairobi da hasken rana da aka saba gani, ind aya fita yin tsalle-tsalle a wani filin shakatawa da ke kusa da gidansa.
Wani zafi da ya afku nan da nan a bayansa ne ya zaunar da shi. Ind abayan wasu 'yan kwanaki ya samu labari, wanda sannan ne tafiya mai wahalhalun da ba a taba tunani ba ta fara.
"An garzaya da ni zuwa asibiti a motar daukar marasa lafiya. Ba tare da bata lokaci ba likitoci suka yi gwajin batiri inda suka fada min cewa ina dauke da nau'kan ciwon daji na myeloma," in ji Kevin wanda a yanzu haka yake matakan warkewa dukka, yayin tattaunawa da TRT Afirka.
A yayin da aka kamu da ciwon daji irin na myeloma da dama, kwayoyin cutar na ciga bargo, inda suke haifar da wasu abubuwa masu taushi a cikin wajen da jini ke samuwa a kasuwanmu.
Wadannan kwayoyin cutar kansa na gurbata kwayoyin halitta na jini. Maimakon su taimaka wajen kare jikin dan adam, sai kwayoyin ciwon dajin su samar da sinadaran da ke bijirewa jiki.
A wannan lokaci Kevin bai san wani abu sosai game da cutar ba. Sai ka ce tunanin yakin makiyin da ba ka iya gani da ke damun jikinsa ba ya razanar da shi, ya san cewa maganin ciwon daji na daukar tsawon lokaci, kuma na da tsada.
"Nan da nan na ji kamar na tsargu, ina tunanin ta yaya wannan cuta farar daya ta girgiza jikina da iyalina. Abu na farko da na ke bukata na yaka shi ne tsarguwa, ba wai cutar daji nai'ina myeloma ba," in ji Kevin.
Zuciya da tararrabi
Duk da birane irin su Nairobi na da kyawawan kayan kula da ciwon daji da farfado da marasa lafiya, amma kuma suna da tsada sosai. Wanna abu dai haka yake a sauran kasashen Afirka.
Mafi yawan mutanen da ake gano wa da cutar na samun karayar zuciya a karon farko. Akwai zabin tafiya kasar waje, musamman zuwa kasashe irin su India, da suke da arhar kula da cutar, amma ko wannan ma abu ne da ba kowa ne zai iya yi ba.
Kamar yadda Kevin ya shaida, wayar da kai da kwnatar da hankalin mara lafiya da danginsa na da matukar muhimmanci wajen yaki da cutar. "Kansa ba tana nufin mutuwa ba, wannan abun da ya kamata a fada wa mutane."
"Idan aka ja hankalin mutane cewa kana da sararin rayuwa sosai idan aka gano cutar da wuri, to ba za su dinga yi wa cutar kansa kallon hukuncin kisa ba."
Kevin ya yi amanna da cewa ba tare da duba da ingancin yanayin kula da cutar ba, hakan ba zai yi aiki ba matukar zuciya ba ta shirya kula da rashin tabbas ba.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Akwai goggona da muka binne a watan d aaka gano ina dauke da cutar, kuma sai na fada wa kaina 'Ba zan karaya ba. Wannan ba zai zama labarina ba.' Na shiga yanayin waraka bayan wahalhalun farko."
Yawaitar kamuwa da cutar
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kamuwa d cutar kansa a Afirka na daduwa sosai.
A 2020, kusan mutum miliyan 1.1 ne suka kamu da cutar kansa a nahiyar. Kusan mutane 700,000 cutar ta kashe.
Almost half of the new cases among adults in Africa are breast, cervical, prostate, colorectal, and liver cancers.
Labari mai dadi shi ne na cewa tsarin kula da lafiya ya taimaka sosai wajen hanzarta yakar yaduwar cutar cikin sauri, tare da kuma yin riga-kafi.
"Muna yaba cigaban da aka samu wajen riga-kafin kansa da magance ta a yankinmu. Misali, kaashe 17 na nahiyar sun sun samar da tsarin tantancewa mai kyau kamar yadda WHO suka bayar da shawara," in Dr. matshidiso Moeti, daraktan shiyyar Afirka na WHO.
Amma baya ga wannan cigaba, sanya mutane su yi aiki da riga-kafin kansa a ka'idojin kula da wadanda ta kama ya zama kalubale.
Kwararru na cewa kasashen Afirka da yawa na baya wajen aiki da ka'idojin riga-kafin ciwon daji da shiga ayyukan gwajin maganin cutar, wand ake kawo koma baya ga ayyukan bincike.
Kevin ya ce ya kamata a tabbatar da jama'a sin ji wannan sako - cewa an samu cigaban binciken kimiyya, kuma an gano ana iya riga-kafin nau'ikan ciwon daji da dama a yau.
"A yanzu, muna da allurar riga-kafin HPV ta kansar bakin mahaifa, amma mutane kadan ne ke zuw akarbar allurar riga-kafin. Ya kamata kowacce mace a Kenya ta zama ta karbi wannan riga-kafin....kowacce yarinya." in ji shi.
Mayar da hankali kan masu kula da lafiya
Kwararrun kula da lafiya na fadin cewa kula da ciwon daji ba iya likitoci, ma'aikatan jiyya da marasa lafiya ya shafa ba kawai.
Kevin ya yarda da cewa ya zama wajibi a samar da tsarin tallafawa. "Ba na tunanin muna yabawa masu kula da lafiya yadda ya kamata, da kuma duk masu taimaka mana a ranakun da muka shiga tsanani," in ji shi.
"Ka zama tare da mutanen da za su karfafa muku gwiwa ba wadanda za su karya maka zuciya ba. Ka nemi masu taya ka raha da za su tallafe ka. Babu sararin tunani mara kyau,' in ji shi yana mai bayar da shawara ga masu yaki da cutar ta kansa.
A tsakanin 2022 da 2024, taken Ranar Ciwon Daji na Duniya da ake gudanarwa duk 4 ga Fabrairu shi ne "Rufe tazarar ciwon daji".
An kammala gangamin da alkawarin matsa lamba ga gwamnatoci su bayar da fifiko ga yaki da ciwon daji. WHO ta bayyana cewa, taken ya hada da neman kasashe su zuba jari wajen riga-kafi da magance ciwon kansa.
Domin karfafa gwiwa da zaburarwa, akwai labarin Kevin - da wasu miliyoyi a duniya da suka yi yaki tare da nasara kan ciwon daji.