Masu fafutikar kare hakkin dan Adam sun dade suna zargin ’yan sanda Kenya da tauye hakkin fararen hula wajen yaki da matsalolin tsaro. Hoto: Reuters

Ga ‘yan kasar Haiti, shawarar da Kenya ta bijiro da ita ta jagorantar rundunar hadaka ta musamman domin dawo da zaman lafiya a kasar ya kasance wani lamari wanda ba sabo ne ba a wurinsu.

Kasar tasu na cikin rikici da kuma rashin zaman lafiya a siyasance. Bayan shafe watanni ana rikici, iyalai sun tsere daga wuraren da gungun masu tayar da tarzoma suke da iko da su.

A daidai lokacin, kungiyoyin ‘yan bijilanti a babban birnin kasar Port-au-Prince sun dauki adduna da sanduna domin kare kansu.

Sai dai sun kasa yaƙar gungun wadanda suke ɗauke da muggan makamai wadanda akasarinsu suka samu daga Amurka, kamar yadda rahotanni ke cewa.

Kungiyoyin ‘yan bindigan sun kuma kashe ‘yan sandan kasar inda suke neman fin ƙarfinsu.

‘Yan bindiga na ta jawo rashin tsaro a Haiti tsawon gomman shekaru. Duk da haka rikicin ya ƙara ƙamari tun bayan kashe shugaban kasar Jovenel Moise a 2021, lamarin da ya bar gibi a shugabancin kasar har ya sa ‘yan bindiga ke rige-rigen neman kujerar.

Rikice-rikicen da ake yi a kasar da suka hada da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya jawo koma baya a bangarori da dama ta bangaren ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi.

A yadda lamura suke, Haiti ta kasa gudanar da zaben ‘yan majalisa bayan wa’adin sanatocin kasar ya kawo karshe.

Duk da rashin doka a kasar, Firaiministan Haiti Ariel Henry na kira ga kasashen duniya da su shiga lamarin domin dawo da doka da oda a kasar.

Ya samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da ƙawayenta.

Kungiyoyin ‘yan bijilanti a babban birnin kasar Port-au-Prince sun dauki adduna da sanduna domin kare kansu

Yadda Kenya ke sauraron kukar Haiti

A halin da ake ciki yanzu, ba a gudanar da sabon zaben wakilan da za su maye gurnin sanatocin kasar ta Haiti wadanda wa’adinsu ya kare tun a watan Janairun da ya gabata ba.

Saboda matsalar da kasar ke fama da ita tayar da kayar bayar ce Firaiministan kasar Ariel Henry ya bukaci taimakon kasashen waje domin tabbatar da bin doka da oda. Ya kuma samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kawayensu.

Ita ma kasar Kenya, bayan shiga wata yarjejeniya da Amurka da ta yi a farkon makon nan da ake ciki, ta amince ta tura ’yan sanda 1,000 domin yaki da gungun masu tayar da zaune tsayen da zimmar samar da zaman lafiya a kasar.

Amma kasar Amurka ce za ta dauki nauyin tura jami’an. Ana jiran sahalewar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kawai kafin jami’an su tafi.

Shugaban Kasar Kenya, William Ruto ya ce gwamnatinsa ta yi hakan ne domin kai wa kasar Haiti agaji bayan nemen agajin da ta yi, sannan ya kara da cewa tura jami’an aikin kwantar da tarzoma, aiki ne na taimakon kasar Haiti a madadin nahiyar Afirka baki daya.

Aikin jami’an ya kunshi taimaka wa jami’an tsaron Haiti wajen yaki da gungun masu tayar da zaune tsaye, da kuma ba ’yan sanda kasar ta Haiti horo na musamman.

“Mun ji kukan ’yan uwanmu maza da mata, kuma lamarin ya taba zuciyarmu,” kamar yadda Ruto ya bayyana a taron Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban Kasar Kenya William Ruto yana shan suka kan zargin amshin shata ga kasashen Yamma.

Matsalolin kasar Kenya na cikin gida

Ministan Harkokin Wajen Kenya, Alfred Mutua ya bayyana wa ’yan jarida cewa akwai yiwuwar nan gaba sauran kasashen Afrika za su shigo lamarin.

Sai dai masana suna bayyana ra’ayoyi mabambanta a kan yunkurin na tura jami’a. Wasu na ganin cewa an yi hakan ne domin kasar Kenya ta samu damar daga darajarta a idon duniya, amma kuma da nufin kare kimar Amurka ta bayan fage bayan an samu rahoton rashin samun isassun dakarun da Amurka za ta dauki nauyinsu a kasar Haiti.

“Akwai kuskure a tsarin. Da farko, ya nuna rashin kwarewa. Na biyu kuma shi ne dogaro da dakarun kasashen ketare,” kamar yadda Farfesa Munene Macharia, wanda kwararre ne kan harkokin dangantaka tsakanin kasashe da diflomasiyya wanda ke zaune a birnin Nairobi ya bayyana a zantawarsa da TRT Afrika.

Ita kanta kasar Kenya tana da matsalar tsaron da take fuskanta a cikin gida, domin ta dade tana fama da hare-haren kungiyar ’yan ta’addar Al-Shabab da ke da yawa a makwabciyarta, Somalia.

A ’yan watannin nan ma hare-haren kungiyar sun ta’azzara, inda aka samu sama da hare-hare 90 a iyakokin kasashen, kuma aka fi kai hare-haren kan jami’an tsaro, da fararen kaya, kamar yadda rahoton cibiyar tattara bayanan rikice-rikice ta Armed Conflict Location and Event Data Project (Acled) ya bayyana.

Martabar kasar Haiti

Masu fafutikar kare hakkin dan Adam sun dade suna zargin ’yan sanda Kenya da tauye hakkin fararen hula wajen yaki da matsalolin tsaro, zargin da su ma suka dade suna karyatawa, inda suke yawan nanata cewa suna bin doka da oda a waje gudanar da aikinsu.

Mutanen kasar Haiti da dama sun nuna rashin amincewarsu da shigowar dakarun kasashen waje. Su kansu shugabannin gungun masu ta da rikicin sun bayyana cewa a shirye suke su yaki dakarun da za a kawo kasar.

Sun ce yakin da bakin dakarun, yaki ne domin kare, “Martabar kasar,” kamar yadda daya daga cikinsu ya bayyana wa ’yan jarida a watan jiya.

Mutanen kasar Haiti sun dade suna zanga-zanga a kan rashin zaman lafiya a kasar a Port-au-Prince 

A aikin kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Haiti na tsakanin shekarar 2004 zuwa 2017, an zargi jami’an dakarun kasashen wajen da take hakkin ’yan Adam, kuma har yanzu wasu mutanen kasar ta Haiti ba su manta wasu cin mutuncin da suke zargi an yi ba.

“A wajen mutanen kasar Haiti, suna kallon lamarin ta fuska biyu ne. Aikin samar da zaman lafiya na baya da aka yi a baya ya bar baya da zarge-zargen tauye hakkin ’yan Adam da sauran kalubale da ake fuskanta idan an tura dakaru,” in ji Adam Bonaa, wanda masani ne a kan harkar tsaro a Afrika da ke zaune a Ghana.

Bambancin harshe

Sai dai ya ce yana da tunanin akwai alamar nasara a gaba, “Za mu ba gwamnatin Kenya da sauran kasashen Yamman lokaci mu gani, muna tunanin watakila wannan karon a samu nasara. Ba za mu yanke kauna da magance matsalolin kasar Haiti ba,” kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika.

Sai dai akwai matsalar bambancin harshe. Kasar Kenya da Turancin Ingilishi ake magana, amma an tura jami’anta kasar da ake amfani da Turancin Farasanci. Masana sun ce wannan zai iya kawo cikas a aikin.

“Ba sa jin yaren Creole na Haiti, kuma ba su san kasar ba sosai,” inji Farfesa Jemima Pierre, wanda dan asalin kasar Haiti ne da ke koyar da tarihi da al’adun Afrika da ’yan Afrika mazauna Amurka a California.

“Kana tunanin kawo dakarun da ba sa jin yaren Haiti sannan ba su san kasar ba sosai zai haifar da da mai ido ne?”

Wasu masu sharhin suna ganin zai fi kyau Kenya ta tura jami’anta kadan, sai kasashen da suke makwabtaka da tekun Caribbean su kawo mafiya yawan dakarun.

Wasu masu sharhin kuma cewa suka yi kasar Haiti ta fi bukatar a tallafa mata wajen inganta jami’anta da kuma inganta tsarin domokuradiyyarta domin ta yaki da masu tada kayar bayar da kanta, maimakon sake tura mata wasu dakarun daga kasashen waje.

TRT Afrika