Daga Abdulwasiu Hassan
"Yauwa NEPA" ne kalamin da ake yi tun da jimawa a Nijeriya, wanda ke nufin rashin kyakkyawan lantarki a kasar.
Idan ka ji wannan kalami a ko ina a kasar da ta fi kowa yawan jama'a a Afirka, to lallai hakan na nufin - cewa an dan kwana biyu ba a gan katsewar lantarki a yankin ba.
Wannan suna na manyan bakake na farkon sunan kamfanin lantarki na Nijeriya ya samu wajen zama a shirin 2024 da aka samar da wannan suna da marubucin fim Ishaya Bako ya yi, wanda ya bayyana tarihin lantarki a kasar ta Yammacin Afirka da irin wahalar da mutane miliyan 200 ke fuskanta.
A sama da mako guda a baya-bayan nan, kusan rabin Nijeriya ya fada ciki n duhu bayan wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun lalata hanyoyin dakon lantarkin a yankunan wasu jihohin arewacin kasar.
Wannan hali ba ya tsayar da rayuwa da kasuwancin mutane a yankin ba ne kawai, har ma da bayyana yadda irin wannan abu ke yawan faruwa a yankunan kasar.
Lambobi ba sa karya
Nijeriya ce kasa ta 10 a duniya mafi yawna arzikin albarkatun mai kuma ta takwas mafi yawan albarkatun iskar gas.
Ka kara da albarktun hasken rana da kasar ke da shi wanda za ta iya samar da makamashin lantarki, kuma babu wani dalili da zai sanya a ce wai ba a samu wutar lantarki a kasar.
Har yanzu, Nijeriya na gwagwarmayar ganin ta samar da lantarki ga 'yan kasar tsawon shekaru.
Manajan Darakta ta Bankin Duniya mai kula da ayyuka, Anna Bjerde, ta bayyana cewa Nijeriya na da mafi yawan mutane a duniya da ba sa samun lantarki.
"Sama da mutane miliyan 85 - sama da 4 daga cikin duk 'yan Nijeriya 10 - ba sa samun lantarki," ta rubuta a wani sako da ta fitar ta shafinta.
"Cewa Nijeriya, kasa ce mai karfin ikon samar da makamashi daga hasken rana, ita ke da gibin lantarki mafi girma a duniya wanda abu ne mai sanya matukar damuwa."
Alkawarun da ba a cikawa
'Yan Nijeriya na wucewa a zamanai daban-daban ba tare da tsayayyiyar lantarki ba, duk da yadda gwamnatocin da suka dinga shudewa sun gaza cika alkawururrukan da suka dauka na kawo karshen matsalar.
Wasu daga cikin muhimman kokarin da gwamnatoci ke yi don magance matsalar karancin lantarki a fadin kasar ciki har da zuba jari a samar da makamashi daga ruwa, iskar gas da hasken rana.
Baya ga wannan zuba jari, kasar ta shaida gyare-gyare da dama da za su inganta bangaren.
A kokarin janyo hankulan masu zuba jari ga bangaren samar da lantarki, gwamnatin Nijeriya ta yanzu ta kara kudin wuta ga jama'ar da ke amfani da ita - ta ware su a matsayin Band A (Rukunin A).
"Domin farfadowar wannan bangare, dole ne gwamnati ta kashe a kalla dala biliyan 10 kowacce shekara a shekaru 10 masu zuwa.
"Ana bukatar samar da kayayyaki matukar ana son bangaren ya farfado, amma gwamnati ita kadai ba za ta iya kashe wadannan kudade ba," in ji ministan lantarki na Nijeriya, Adebayo Adelabu.
"Dole ne mu mayar da wannan sashe mai janyo hankalin masu zuba jari da masu bayar da rance. Kuma hanya daya da za a iya jan hankalin shi ne samar da farashin kasuwa," in ji shi.
Masu amfani da lantarki na Rukunin A (Band A), wadanda ke da alhakin biyan kudade da yawa, na cewa karbar kudade da yawa daga hannayensu bai bayar da ma'ana ba saboda lantarkin ta ragu.
Durkushewar masamar lantarki ta kasa
Nijeriya na samar da kimanin megawatt 6,000 na lantarki ga 'yan kasar su sama da 200, wanda adadi dan kadan idan aka kwatanta da megawat 48,000 ga mutanen da ba su wuce miliyan 60 ba.
Kwararru na bayyana yawaitar durkushewar cibiyar bayar da lantarki ta kasar ga rashin isasshen samarwa da rarraba lantarkin.
"Raguwar samar da lantarki fuju'an na iya rikita tsarin gaba daya, yana mai iya janyo durkushewar sa gaba daya," Dr Abubakar Ibrahim, wanda ya samar da kamfanin Enpower Energy Consult, ya shaida wa TRT Afrika.
Ya bayyana lalata hanyoyin dakon lantarki da tsufan injina, ciki har da transformer da sauran kayan tashoshin, wanda su ne musabbabin mummunan halin da sashen lantarki ya tsinci kansa a ciki.
"Kididdiga ta nuna cewa daga watan Janairu 2024 zuwa yau, an lalata hasumiyoyin dakon lantarki 66 a Nijeriya, na baya-bayan nan ita ce 33KV Lokoja-Gwagwalada a ranar 9 ga Nuwamba. An lalata hasumiyoyi uku, sannan an sace karafan an tasfi da su," in ji Dr. Ibrahim.
Mafita
A yayin da gwamnati ke jiran masu zuba jari a bangaren lantarki, shin akwai yiwuwar fita daga wanan kangi na duhu a fada haske?
Bjerde ta yi amanna da cewa dole ne kasar ta mayar da hankali kan makamashi mai sabuntuwa ba wanda hakan zai sanya ta magance matsalar.
Ta ce "Gwamnatoci, muna fara wa da ta Nijeriya, na bukatar yin jagoranci wajen samar da makamashi mai tsafta ta hanyar yin sauye-sauye kan manufofi tsayayyu da dokoki, wadanda za a samar da kudaden tabbatar da su wadanda za su janyo hankulan 'yan kasuwa masu zaman kan su su zuba jari."
Tunda an riga an sayar da kamfanin samar da lantarki a Nijeriya, an kauce hanya wajen tabbatar da dokokin da aka gindaya.
Sai dai kuma, a wajen kwararru masu bayar da shawarwari kan lantarki irin su Dr Ibrahim na cewa mafita din ta wuce ga samar da tsaftataccen makamashi mai sabuntuwa.
"Akwai bukatar zamanantar da tsarin samarwa da rarraba lantarkin, a inganta kula da injina da kayan aiki, sannan a samar da wuraren samar da lantarki a yankuna daban-daban." ya fada wa TRT Afrika.
"Masamar makamashi mai sabuntuwa kamar hasken rana, iska da ruwa, wadanda ana da su da yawa a arewacin Nijeriya, za kuma su rage nauyin da ke kan masamar lantarki ta kasa."
'Yan Nijeriya sama da miliyan 85 da ba sa samun lantarki za su yi fatan cewa ba za a daina kokarin da ake yi na nemo mafita mai dore wa ba.