Daga Sylvia Chebet
Wata doguwar hanya ce mara kwalta a gaban Esther Njeru, yayin da hasken rana ke sauka kan fuskarka.
Tsohuwar mai shekara 65 na tafiya cikin sauri, dauke da jarkarta mai nauyin lita 20 wadda babu komai a cikinta, tana sa ran cika ta da ruwa a hanyarta ta dawowa.
Esther ta shafe shekaru da dama tana yin haka - tana tafiyar kilomitoci don ɗiban ruwa daga koguna don biyan buƙatun iyalinta.
Wahalhalun yau da kullum da Esther da al'ummarta ke fuskanta a gundumar Tharaka Nithi da ke yankin tsakiyar Kenya sun zo karshe.
Ayyukan shirin eWATER da ke zaman kansa ya samar da rijiyoyin burtsatse da dama a yankin da Esther ke zama, a matsayin wani yunƙuri na aikin samar da tsabtataccen ruwa mai rahusa ga mazauna yankunan karkara a Kenya.
Ana tara ruwan da aka zuƙo daga rijiyoyin burtsatse zuwa manyan tankuna, kana sai a kashe duk wasu cututtukan da ke ciki, daga nan kuma sai a zubo ta fasahar famfon hasken rana da aka samar.
Famfunan suna aiki ne ta hanyar tsarin biyan kudi da aka kirkiro na IoT ko kuma ta hanyar fasahar intanet na abubuwa.
''Al'ummar yankin Tharaka Nithi suna samun ruwan amfani ba kamar da ba. Wannan aikin zai sauya rayuwarsu sosai,'' kamar yadda Elisha Omega, injiniyan da ke aikin samar da fasahar ruwa na eWater ya shaida wa TRT Afirka.
Tsarin biyan ƙudi
Ta hanyar amfani da wayoyin zamani, masu amfani suna siyan eWater Credit ne sannan su samu ruwa mai tsabta ta hanyar latsa alamar maganadisu.
"Mun ziyarci al'umma da dama, muna yi musu bayani kan yadda wadannan famfuna suke aiki," in ji Omega.
Esther na daga cikin mutane da dama wadanda aka karon farko suka taba shaida irin wannan sabuwar fasaha da aka yi masa lakabi da '' Fasahar famfo na farko wato eWater.''
Ta zare wani kati mai dauke da wani shudin tambari na maganadisu, wanda ta manne akan fasahar da ke jikin famfon, nan take sai ruwa ya soma fitowa.
''Tsarin yana aiki ne nan take, ba ya ɓata lokaci bare a yi asarar ruwa idan famfon ya ɓude kuma yana rufewa nan take,'' in ji Omega.
Ya kuma kara da cewa "Za ku samu wani lambar shaida ta musamman, wadda shi ne shaidar asusunku…Don haka, da zarar akwai kuɗi a cikin katin, sai a sanya shi a kan famfo, nan take zai samar da ruwa."
Yaduwa zuwa ko ina
Wannan shiri na samar da ruwa mai ɗorewa zai mayar da hankali ne wajen samar wa mutane miliyan daya ruwa a Kenya daga yanzu zuwa shekarar 2029.
Faith Makena, wacce gidanta ke da nisan mita 200 daga wuri mafi kusa da fasahar famfon eWATER, ta samu kwanciyar hankali inda take da tabbacin samun ruwa mai tsabta a kusa ba tare da yin tafiya mai nisa ba.
Kafin zuwan wannan ci gaba da aka samu, takan sayi ruwa mara tsabta daga masu sayarwa, inda take biyan kwatankwacin dalar Amurka daya akan jarkoki takwas masu daukar lita 20.
A farashi iri daya yanzu tana samun isasshen ruwan da za ta cika irin wadannan jarkoki har 30.
"Ina amfani da ruwan wajen wanke-wanke da dafa abinci da sha da kuma biyan duk wasu bukatuna na gida," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Tabbacin tsabtatacen ruwa
Zacharia Njeru, sakataren majalisar zartarwa kan ruwa na kasar Kenya, ya tabbatar wa al'ummar kasar a yayin kaddamar da aikin cewa abin da suke samu tsabtataccen ruwa mai inganci ne ta hanyar amfani da hanyoyin kimiyya.
Gwamnan gundumar Tharaka Nithi, Muthomi Njuki, ya yi imanin cewa aikin zai yi matukar tasiri ga lafiyar al’ummar yankin.
"Cututtukan da ake samu a ruwa mara tsabta da ɗimbin jama'a ke tururuwa zuwa ɗiba a Nkodi da sauran wuraren a fadin Tharaka Nithi zai zama tarihi," in ji shi.
"Kada kowa ya yi kokari sauya muku tunanin kar ku siya ruwan, za su fada muku cewa, za ku iya ajiye shilling biyu ta hanyar debo ruwa daga kogi, amma karya ce kawai cuta kawai za ku siya wa kanku.''
Ana amfani da kudin cajin da ake karba wajen kula fda gyaran ruwa "Idan wani bututu ya fashe ko famfo ya lalace kuma ana buƙatar a canza shi, a koyaushe za a samu kuɗin aikin kula da hakan," in ji Omega.
"Wasu na'urori da aka hada fasahar famfon da su kan shaida mana idan akwai wata matsala, watakila idan yoyo ko kuma famfon ya daina aiki. nan take za a samu mafita daga tawagar injiniyoyin da aka tanadar''.
Babban nauyi kan jinsi
A cewar hukumar dake kula yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, mata da yara 'yan mata a duniya baki daya suna kashe sa'o'i miliyan 200 wajen diban ruwa a kullum, wani bangare da ba a la'akari da shi.
Ga yara mata, zuwa ɗiban ruwa wa iyalansu aiki ne babba da ba a biya, kuma hakan na nufin rage musu lokutan zuwa makaranta ko kuma daina fita gaba ɗaya.
Ga mata su kuma, bata lokaci akan wannan aiki na yau da kullum na nufin rba za su samu isasshen lokuta masu ma'ana da su iya tabuka wani abun yi na kasuwanci ba. wanda hakan na kara musu raunin fuskantar talauci.
As Makena parts ways with her neighbour Esther, their backs hunched forward under the weight of the containers they each carry, a new dawn beckons with the promise of a life less burdensome.
Yayin da Makena ke raba hanya da makwabciyarta Esther, bayansu dauke da jarkokin ruwa da suka dauka, wani sabon alfijir ne ya bullo tare da alkawarin sauya musu rayuwa cikin sauki.