Direbobin tasi a Kenya na neman ƙara yawan kuɗin mota don su samu damar sayen man da zai ba su damar biyan buƙatun mutane. / Hoto: AFP

Daga Sylvia Chebet

Ku kalli wannan. Ka tafi filin jiragen sama, tashar jiragen ƙasa ko babbar tashar motocin bas da aka samar a wani sabon waje, mene ne abu na farko da za ka yi? A mafi yawancin lokaci, abin da matafiya suka fi yi shi ne yabon direbobin tasi.

Kuɗin motar, wanda ake biya duba da nisan wajen da za a je, lokacin zuwa da yanayin tattalin arzikin wajen, shi ne babban alƙawarin da ke tsakanin direba da fasinja a tsawon tafiyar da za a yi.

A Kenya, inda a baya-bayan nan aka yi zanga-zangar adawa da ƙarin haraji, wanda ya sake lalata tattalin arziki, direbobin tasi na cikin tsaka-mai-wuya.

Idan suka ƙara kuɗin tasi to za su rasa kwastomominsu waɗanda za su koma wajen manyan kamfanonin tasi. Idan suka ci gaba da karɓar kuɗin da suke karɓa a yanzu, za su yi ta kasancewa cikin asara.

Tsananin gogayya tsakanin kamfanoni ƙanana da manya na zamani irin su Uber da Bolt ya janyo raguwar farashin kuɗin ababan hawa na haya ta yadda har babu wani amfani da ake samu, in ji direbobin tasi na gargajiya.

"Kamar ɗebo ruwa ne a cikin kwando," in ji direban tasi Samson yayin tattauna wa da TRT Afirka.

Wannan hali da ake ciki ba mai ɗore wa ba ne ga direbobin da ake biyan basussuka, sayen abinci, da biyan kuɗin makaranta da kula da lafiya.

Wata mace direba ta ce bata iya ajiye komai bayan biyan shiling 2,000 na Kenya, kwatancin dalar Amurka $15 kuɗin bashin motarta.

"Ina da 'ya'ya da ke zuwa makaranta, kuma da kuɗin haya da na ke biya," in ji ta. "Kana aiki ne inda ake samun shiling 200, inda bayan awanni 12, za ka ga ba ka samu isassun kuɗin da za ka biya bashin motar taka ba ko ka sayi mai. Abubuwa ba sa tafiya daidai, kuma ba mu da wata hanya," in ji ta, tana bayani kan irin ƙarin kuɗaɗen da sauran kamfanoni ke ƙara wa a kan kudin mota.

Kuɗaɗen da ake kashewa

Kenya ɗaya ce daga ƙasashen da kamfanonin ababan hawa suka yawaita. Yawan jama'ar kasar na ta ƙaruwa, amma mallakar motcin yana raguwa, wanda shi ne ke haɓaka kasuwancin motocin haya.

Kamfanonin na samun kiran mai son hawa mota a kowace sa'a, kuma suna da dama kan fasinjojin da dole ne su yi aiki da kuɗin da yake a rubuce.

Domin kasuwancinsu ya zama mai amfani ta fuskar tattalin arziki, direbobin sun yi shawarar ƙara kuɗin da ake biya daga shiling ɗin Kenya 150 zuwa 200 ga mota karama da ke ɗaukar mutane uku, da kuma shiling 300 ga mota da ke ɗaukar mutane da yawa.

A daya gefen kuma, direbobin sun ƙara rabin kuɗin motar da suke cajin fasinja, ma'ana za su caji shiling 300 a tafiyar shiling 200.

"A lokacin da aka takura ka zuwa bango, kai ma sai ka tura na gabanka," in ji wani direban tasi. Wasu fasinjojin ma na biyan kuɗi da yawa. Wasu kuma ba sa bayarwa da yawa, suna barin direbobin da zaɓin karɓar kuɗi kaɗan.

A wajen wani direba, yana ganin ya kamata direbobi su dinga lissafa man da suka ƙona yayin zuwa wani waje, a wasu lokutan kuma su nemi ƙarin kuɗi daga wajen fasinja, abin da a wasu lokutan ana dade wa a hanya saboda cunkoso.

"Idan ka samu kira kamar sau biyar wanda ke sanya ka dole ka yi tuki mai nisan kilomita 10 don ɗaukan fasinja, idan man da motar ke sha ya kai shiling 20 duk kilomita 1, kenan za ka shan man shiling 200 a kowacce tafiya."

Idan aka haɗe kuɗin baki ɗaya, za ka ga ka kashe shiling 1,000 ($7.75) don ɗaukar fasinja, in ji wani direba.

Yadda kuɗin man da ake ƙonawa kafin a ɗauki fasinja ke faɗawa kan direba, za su dinga cutuwa ne musamman idan suka shiga cunkoson ababan hawa bayan sun dauki kwastomansu - wand abu ne da ake gani kullum a lokacin gaggawar fita ko dawo wa daga aiki.

Manhajar na yanke wani kaso daga kuɗin da kwastoma ya biya. Saboda haka yankar kashi 20 daga wannan tafiya zai bar direba da 'yan kuɗaɗe a hannunsa kawai.

"Ka tuna idan aka ce ka rasa shiling 80. Wanne irin kasuwanci ne wannan?" in ji Samson.

Yanayi mai wahala

Wasu direbobi kaɗan na karɓar bashi su sayi motoci, inda sauran kuma suke daukar haya. Idan sun tashi aiki kullum, ana tsammanin su biya kudin da aka yi yarjejeniya da su ga mai motar bayan cire kudin mai da sauran su.

Mafi yawan direbobi suna biyan shiling 2,000 mafi ƙaranci, ya danganta da girman motar.

"Kamar yadda aka saba motar na da na'urar auna nisan tafiya da inda aka je, hakan na nufin duk motsin da ka yi, mai motar ya san ina ka je saboda yana bibiyarka, kuma ya san kudi kake samu. Saboda haka suna sa ran karbar kudade saboda motar na ta yawo," in ji Samson.

Akwai wasu ƙalubale da yawa, kamar dakatarwar ta-ci-barkatai, dan barazana da mummunar mu'amala daga kamfanonin ababan hawar, da ma cin fuska daga wasu fasinjojin.

"Da zarar sun dakatar da kai, sai batun ya zama na Hukumar Sufuri da Tsaro ta Ƙasa. Da wahala a iya sabunta takardun tuki na wanda hakan ta sama. Kenan an kore ka daga sana'ar baki ɗaya." in ji Samson cikin takaici.

neman mafita

Wani kamfanin motocin haya a Kenya, mai suna Little Cab, na ta ƙoƙarin tabbatar da ba a dora wa direban nauyin duk wata asara ba.

Samson ya kara da cewa "Suna iya kiran direba. haka kuma, za ka iya kiran su, ka tura sakon email ko sako ta wayar hannu a duk lokacin da kake da wani korafi da kake son mika wa."

Wani kamfanin mai suna Faras Cabs, na daukar matakan kare hakkokin direbobin tasi da fasinjoji a lokaci guda.

"Mun kawo wasu 'yan sauye-sauye da za su taimaka wa direbobi a lokacin da kuma ake samarwa da fasinjoji sauki su ma. Abu na farko da muka yi shi ne ƙara yawan kuɗi mafi kankanta daga shiling 200 zuwa 240," in ji Osman Abdi, shugaban sashen kasuwanci na kamfanin Faras Cabs.

Direbobin tasi na jiran ganin ko manyan kamfanonin tasi da suke aiki a ƙasashe daban-daban za su biyo sahunsu.

Wani direban tasi na nuna manhajar biyan kudin tasi ta hanyar amfani da wayar hannu tare da katin banki a Mexico City.

TRT Afrika