Daga Coletta Wanjohi
Kimanin 'yan Sudan mutum 90,000 ne ke samun mafaka a kasar Habasha a halin yanzu, bayan da suka tsallaka kan iyakar kasar cikin rukuni daban-daban tun bayan soma kazamin fadar da ta barke tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF a watan Afrilun bara.
Yawancin wadannan 'yan gudun hijirar suna zama ne a sansanoni mabambanta.
Ana sa ran samun wasu karin 'yan Sudan wadanda suke neman mafaka yayin da kokarin kungiyar Ci-gaban kasashen Gabashin Afrika takwas wato IGAD ke yi na shiga tsakani wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban gwamnatin rikon kwaryar Sudan, da shugabandakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya ci karo da tsaiko.
A baya-bayan nan ne Sudan ta sanar da matakin dakatar da matsayinta na zama mamba a kungiyar IGAD, tare da nisanta kanta daga halartar babban taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar da za a yi a Kampala a ranar 18 ga watan Janairu.
Ficewar Sudan daga kungiyar na zuwa ne bayan zagin da gwamnatin riƙon ƙwarya ta yi wa IGAD kan cewa ta sanya rikicin Sudan cikin muhimman batutuwanta ba tare da an tuntubar ta ba.
Bayan ga Sudan, kasashen da suka hada kungiyar IGAD sun hada da Djibouti da Habasha da Kenya da Somalia da Sudan ta Kudu da Eritrea da kuma Uganda.
"IGAD ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani tare da samun goyon bayan fararen hula na Sudan da kungiyoyin siyasa daban-daban.
Yanzu da Sudan ta juya bayanta ga kungiyar, akwai yiwuwar hakan ya kawo cikas ga tsarin tare da jinkirta komawanta ga gwamnatin farar hula,'' kamar yadda Nuur Mohamud Sheekh, tsohon kakakin kungiyar IGAD, ya shaida wa TRT Afrika.
Taron IGAD da aka gudanar a makon da ya gabata ya bai wa janar din biyu da ke fada da juna kwanaki 14 su gana ido-da-ido domin kawar da halin rikicin da ake ciki, lamarin da ya kara fusata Sudan.
"Sudan ta ƙaurace wa taron, sannan sanarwar karshe a taron na kunshe da kalamai da kasar ke ganin rashin mutunta yancinta ne da kuma cin zarafi ne ga iyalan wadanda rikicin 'yan tawayen ya rutsa da su,'' a cewar wata sanarwa da gwamnatin gudanarwa ta Sudan ta fitar.
A taron da suka yi a watan Disamba na shekarar 2023, shugabannin kasashen IGAD sun samu tabbaci daga al-Burhan da Dagalo cewa za su hada kai domin yin aiki da yarjejeniyar zaman lafiya.
Rikicin jinƙai
Matakin da Sudan ta dauka na baya-bayan nan ya haifar da fargabar kan yiwuwar fadan ya kara kazanta, lamarin da ke kara jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali tare da kara yawan masu gudun hijira.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya MDD, sama da mutane miliyan 7.6 ne suka rasa matsugunansu tun bayan barkewar fadan a ranar 15 ga Afrilun bara, adadin da ke ci gaba da karuwa.
''Adadin mutanen da suka rasa matsuguninsu a Sudan ya karu da kusan mutum 19,600 a makon da gabata,'' a cewar sanarwar da Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a ranar 21 ga watan Janairu.
Kazalika, yakin yana shafar makwabtan Sudan. "Fadan ya haifar da wani tashin hankali da rikici na jin kai a gabashin kasar Chadi, inda kusan mutane rabin miliyan suka samu mafaka, tare da al'ummomin da tuni suke cikin mawuyacin yanayi da kuma dubban 'yan gudun hijirar Sudan da suka kwashe shekaru sama da ashirin a kasar," in ji Kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF).
A Khartoum babban birnin kasar kuwa, asibitoci kalilan ne suke aiki a halin yanzu, kuma farashin magunguna na ci gaba da hauhawa.
Rikicin ya kara wa hukumomin agaji wauyan iya kai taimakonsu ga mutane, musamman a yankunan da RSF ke da iko.
Rashin Hasashe
A ranar 6 ga watan Yuni shekarar 2019, aka dakatar da Sudan daga kungiyar Tarayyar Afirka "har sai sanda kasar ta kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula".
Yayin da gwamnatin rikon kwarya ta Soji a kasar ta sanar da cewa, za a gudanar da babban zabe a shekarar 2024, lokacin da ake ganin ya yi nisan zuwa mussaman la'akari da ficewar kasar daga kungiyar IGAD.
Wasu masana sun ce watakila akwai tasirin muradun kasashen waje a shirin samar da zaman lafiya a Sudan, kuma da alama shugabannin kasashen IGAD da AU na cikin tsaka mai wuya wajen tunkarar rikicin.
Moussa Faki Mahamat, Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, ya nada wani kwamiti mai mutane uku da zai fara kokarin kawo karshen rikicin siyasa da na soji da ake ciki a halin yanzu.
Kwamitin zai yi aki tare da dukkan masu ruwa da tsaki a Sudan da kungiyoyin yankunan da na kasashen duniya, ciki har da IGAD da MDD da kungiyar kasashen Larabawa.
Wasu manazarta na ganin cewa daukar matakin nisanta kanta daga IGAD da Sudan ta yi babban kuskure ne, lamarin da kara kebe janar al-Burhan da kasarsa.
Wasu kuma na ganin hakan a matsayin wani gwaji na hakurin kungiyar kasashen yankin gabashin Afirka, wacce aka sake watsa wa kasa a ido bayan da Habasha ta ki halartar taron kolin da aka gudanar da Kampala a ranar 18 ga watan Janairu, saboda rikicinta da Somaliya, kan batun yarjejeniyar musayar hayar bakin teku mai nisan kilomita 20 da samun yancinta.
Saboda 'yan Sudan miliyan bakwai da aka tilastawa barin matsugunansu da kuma miliyoyin wasu da ke zaune a bakin teku, IGAD ba za ta iya yin kasa a gwiwa ba.