Wani nazarin jin ra'ayin jama'a a fadin duniya da aka yi ya bayyana cewa mafi yawan wadanda suka amsa tambayoyi a nazarin sun bayyana cewa an tsara manhajojin sadarwa ne su zama ana amfani da su a koyaushe.

Daga Halima Umar Saleh

Ziya'atulhaqq Tahir, wata mai fitar da bayanai a shafinta na yanar gizo daga arewacin Nijeriya, tana da amsar kusan dukkan tambayoyin da suka shafi rayuwa.

A shafinta na Instagram mai mabiya da yawa, mabiyanta na fito wa ƙarara su bayyana matsalolinsu - tun daga alaƙar miji da mata zuwa wajen aiki - suna neman shawarwarin yadda za su tunkari matsalolin.

Ziya'atulhaqq na bayar da amsa da kanta ga waɗannan batutuwa ko ta nemi shawarar sauran mabiya shafin nata.

Ta yi suna sosai a matsayin wata antin intanet da ake kai wa koke, kuma daga cikin koken akwai na cin zarafi a shafukan sada zumunta. Wata rana, ta goge shafin nata. Da fari na tsawon watanni uku, daga baya har tsawon shekara guda da watan biyu.

"Ina daf da yin aure, kuma cin zarafi da barazana ta intanet ba ni kadai yake damu ba har ma da iyalina," ta shaida wa TRT Afirka.

A wata gaɓa, cin zarafin ya tsananta inda har ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwar Ziya'atulhaqq.

Alkaluman shafin Statista sun bayyana cewa amfani da fasahar zamani ya ƙaru sosai a Afirka, inda ya zuwa karshen 2023 mutum miliyan 645 a nahiyar suke samun amfani da intanet.

A yayin da wannan sauyi a fagen sadarwa ya inganta harkokin isar da saƙonni da damarnmakin tattalin arziki, ya kuma zo da kalubalen walwala, ciki har da zama lafiya a intanet, sanin me ya kamata a yi a intanet da mummunan tasirin shafe lokaci mai tsawo a kan allon na'ura.

Ziya'atulhaqq ta yi kokarin dawowa sahar bayan shekaru da fuskantar cin zarafi a intent wanda ya sanya mata damuwa, amma ba duk wanda aka zalunta a yanar gizo ba ne yake iya sake komawa.

A Nijeriya, cin zarafi a yanar gizo na daya daga batutuwan da ke damun jama'a a wannan zamani na bunkasar yanar gizo. "Azzaluman ba su da iyaka. Suna kai wa kowa hari, ba tare da duba ga wanda suke ƙuntatawa ba. Ina jin takaici sosai a lokacin da suka yi wa wani da nake ƙauna; Na kasa jurewa."

"An kirkiri shafuka sama da 30 a shekara uku don a zalunce ni, an raba ni da duk wani farin ciki tare da sanya ni tambayar me ya sa ma nake raye. Wannan abu na sanya mutum tunanin kashe kai da mummunar matsalar damuwa, yanayin da nake fama da ita har yanzu."

Tattaunawa mai wahala

Daga cikin abubuwan da ke kusa da zuciyar Ziya'atulhaqq shi ne bukatar sake fara tattaunawa a duniya don saka dokokin amfani da kafafen sadarwa, musamman a Afirka.

Ziya'atulhaqq ta yi kokarin dawowa sahar bayan shekaru da fuskantar cin zarafi a intanet ya sanya mata damuwa

A wajen wani taro da aka yi a baya-bayan nan a garin Dammam na Saudiyya, Cibiyar Raya Al'adu ta Sarki Abdulaziz da ke gabatar da shirin Sync, an tattauna kan shirin da ake yi don rage illar tasirin fasahar kere-kere a Afirka.

"Sync zai wayar da kan jama'a a Afirka ta yadda za su san illolin da ke tattare da yawan amfani da shafukan sada zumunta," in ji Fahad AlBeyahi, jagoran kula da shirin inganta amfani da intanet na cibiyar.

Cibiyar na da manufar shirya Babban Taron Zaman Lafiyar Amfani da Intanet a Afirka, inda masu ruwa da tsaki a nahiyar da shugabanni da gwamnatoci za su hadu don tattauna tasirin hanyoyin sadarwa na zamani, kusa duk a kan zama kalau da tsaro.

Ziya'atulhaqq na ganin wannan a matsayin tunani mai kyau kuma hakan ya zo a lokacin da ya dace. Ta fada wa TRT Afirka cewa "A nahiyar ba a tattaunawa kan irin wadannan batutuwa tare da magance su, duk da suna saka rayukan miliyoyi a cikin hatsari. Ana bukata cikin gaggawa a yi dokokin yakar cusgunawa a intane, musamman a Nijeriya inda lamarin ya zama ruwan dare."

Munanan sakamako

Kristin Bride wadda na daga cikin manyan masu jawabi a wajen taron Sync, na tsoron zuwa ranar 23 ga Yuni saboda wannan ranar ce ɗanta zai cika shekara guda da kashe kansa bayan fuskantar cin zarafi a intanet.

Kristin mai rajin ilmantar da mutane kan cin zarafi a intanet da kuma irin rawar da shafukan sadarwa na intanet ke taka wa a rayuwarmu, ta gano cewa a 'yan kwanaki kafin danta Carson ya mutu ya karbi daruruwan sakonnin barazana ta wata manhaja d ake baiwa masu amfani damar boye ko su waye su.

A lokacin da Kristin ke bayar da labarin yadda danta ya kashe kansa saboda cin zarafinsa a intanet, kusan kowa a wajen taron ya shiga damuwa. / Hoto: Ithra

Tarihin amfani da waya na Carson ya bayyana ya sanya an dade ana binciken wanda ke da hannu wajen aika masa wadannan sakonni na cin zarafi a yanar gizo, da kuma tattauna me ya kamata a yi don kawo karshen hakan.

"Wannan abu na faruwa tare da iyalai da dama a Afirka. yanzu ne lokacin a tashi tsaye a yaki cin zarafi a yanar gizo da sauran illolin da fasahar kere-kere ke janyo wa." in ji Ziya'atulhaqq.

A wajen taron na Dammam da aka kammala, AlBeyahi ya kawo alkaluma daga nazarin tambayoyin da aka yi wa mutum 35,000 'yan sama da shekara 18 a kasashen duniya 35 da ke nahiyoyi biyar, ciki har da kashen Afirka shida.

Sakamakon nazarin ya bayar da karin haske kan batutuwa shida masu alaƙa da juna; kamar daidaito da Kirkirarriyar Basira da shafukan sadarwa da wasannin gem da aiki da dokoki.

Daya daga cikin bangarorin alkaluman mai muhimmanci shi ne yadda ake tsara shafukan sada zumunta na intanet. Kusan kashi 73 na wadanda suka amsa tambayoyin sun ce an tsara manhajojin ne ta yadda za su zamar wa mutum alaƙaƙai, inda kashi 52 suka nuna damuwa game da lafiyar kwakwalensu saboda tasirin shafukan sada zumunta.

Aisha Falke, wata mai wallafe-wallafe a intanet a Nijeriya, na da ra'ayin cewa an tsara manhajojin ne ta yadda za su zamarwa mutum alakakai.

An fitar da sakamakon nazarin da Ithra suka gudanar a wajen taron Sync 2024. / Hoto: Ithra

"Yawan amfani da fasahar sadarwa a Afirka ya tsnaanta, kamar yadda yake a sauran sassan duniya, duk da cewa samun su ba kamar a sauran kasashen da suka ci gaba ba.

"Muna ganin yadda mutane da fasahar sadarwa ta zamo musu alakakai suke fuskantar mummunan sakamako a ɓangarori daban-daban na rayuwa, ciki har da alakarsu da iyalai, aiki ko kokari a makaranta da ma jin dadin rayuwarsu," in ji ta.

Alkaluma kan wasannin gem na yanar gizo na sanya damuwa ga Hassan Abubakar, wanda yaronsa ɗan shekara 14 ya zama mai maitar yin wasan "kuma duk wani yunkuri na hana shi ya gagara aiki".

Ayisha Piotti, mai jawabi a wajen taron Sync, ta shawarci iyaye da su dauki mataki tun kafin lamarin ya munana yadda ba za su iya shawo kansa ba.

"A matsayin iyaye, kuna da zabi biyu - ko ku bari su yi ko ku ce 'zan taka rawa a wannan bangare na rayuwar yarana da makomarsu a nan gaba'."

TRT Afrika