Daga Abdulwasiu Hassan
A daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ke bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai a ranar 30 ga watan Yuni, tana kuma cika shekaru 65 da soma rikici a cikinta da fama da talauci da kuma wahalwalun da ta samo tun daga mulkin mallaka.
Sai dai hakan ya ta’allaka ne kan irin labaran da ake samu daga gidajen jaridu dangane da ƙasar.
Ga wasu abubuwan da watakila ba ku sani ba masu kyau game da ƙasar wadda ake yawan yaɗa labarai marasa daɗi a game da ita:
Faɗin ƙasa
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ce ƙasa ta biyu mafi girma a faɗin ƙasa a Afirka bayan Aljeriya inda take da murabba’in kilomota miliyan 2.345.
Kusan kashi 60 cikin 100 na Yammacin Turai kenan wanda ya haɗa da Faransa da Jamus da Sifaniya da Birtaniya da wasu ƙananan ƙasashe.
Galibin ƙasar tana cikin Kogin Kongo kuma tana alfahari da dazuka da tsaunuka.
Fitar da man fetur
DRC ƙasa ce da ke samar da man fetur inda take da narkakken man fetur a cikin ƙasa da ya haura ganga biliyan biyar.
Kamar yadda wata ƙididdiga da OEC World ta fitar, ƙasar ta samu dala miliyan 916 a 2022 ta hanyar fitar da man fetur.
A halin yanzu dai an takaita hako man da kasar ke yi a gabar teku, inda ake fitar da ganga 25,000 a kowace rana, wanda kuma ake fitar da shi zuwa kasashen waje.
Tafkin Kivu, wanda ya ratsa ta cikin DRC da Rwanda da Burundi, an kiyasta cewa yana ɗauke da narkakken methane kusan kubik biliyan 60, wanda za a iya amfani da shi wajen samar da wutar lantarki.
Samar da lantarki ta ruwa
Hanyar samar da lantarkin ƙasar Kogin Congo ne. Kogin ne na biyu mafi girma a Afirka, na uku kuma mafi girma a duniya.
An yi ƙiyasin cewa kogin na da ƙarfin samar da megawatts 100,000 na lantarki.
A cewar kungiyar Tarayyar Afirka, a halin yanzu DRC tana da kashi 13 cikin 100 na ƙarfin samar da lantarki daga kogi a duniya.
Hukumar wutar lantarki ta ƙasar Kongon ta ce tana sa ran nan da shekarar 2025 aƙalla mutum miliyan 15 su samu wutar lantarki a ƙasar.
Arzkin jan ƙarfe
DRC ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da arziƙin jan ƙarfe, wanda yake da matuƙar amfani wurin haɗa wayoyin da ake amfani da su a aikin lantarki.
Haƙar jan ƙarfe a ƙasar ana yin sa ne a can yankin da ake da arziƙinsa na kudancin lardin Katanga.
Wurin da ke da wannan arziƙin na da faɗin kilomita 70 da kuma tsawon kilomita 250, tsakanin Lumumbashi da Kolwezi.
Ba abin mamaki ba ne, jan ƙarfe na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke samar wa Kongo kuɗin shiga.
A cewar OEC World, kasar ta samu dala biliyan 16.3 daga jan ƙarfen da aka fitar a shekarar 2022.
Arziƙin Cobalt
Haka kuma Kongo ta kasance ƙasar da ke da arziƙin cobalt, wanda ake amfani da shi wurin haɗa abubuwa da dama na zamani.
Cobalt na da amfani sosai wurin haɗa batirin da ake cazawa musamman batiran waya da kwamfuta da motocin lantarki.
Haka kuma Cobalt wani sinadari ne da ake amfani da shi wurin samar da sinadarin Vitamin B12, wanda ke taka muhimmiyar rawa a jikin bil’adama da dabbobi.
DRC ce ke samar da kashi 70% na cobalt ɗin duniya. Bisa la'akari da tattalin arziki da sauran hasashe, da alama hakan zai ci gaba da kasancewa har sai an samu karuwar hako ma'adinai a kasashe daban-daban.
Arziƙin Coltan
DRC ce ƙasar da ke kan gaba wurin samar da coltan a duniya, wanda wani dutse ne baƙi.
Abubuwa biyu da ake cirewa daga coltan su ne niobium da tantalum – waɗanda ke taka muhimmiyar rawa a wurin kimiyya ta zamani, da haɗa wayoyin hannu da kwamfutoci da lantarki na mota da kuma kemarori.
Arzƙin lu'u-lu'u
Kongo na daga cikin ƙasashen da aka bayyana waɗanda ke kan gaba wurin samar da lu'u-lu'u a duniya.
Tshikapa na da nisan kusan kilomta 50 daga arewacin iyakar Angola, wanda ke kan iyakar Kasai kimanin kilomita 50 daga arewacin iyakar Angola, an amince da shi a matsayin gundumar hakar lu'u-lu'u na DRC.
Tun lokacin da aka gano lu'u-lu'u na farko a yankin a cikin 1907, yankin ya fuskanci sauye-sauye na tsari yayin da ya kasance wani muhimmin bangare na masana'antar dala biliyan 81.4.
Arziƙin zinare
Wannan kasa da ke yankin tsakiyar Afirka na da arziƙin narakakken zinarin da aka ƙiyasta cewa ya kai dala biliyan 28.
Duk da cewa hakar gwal a DRC har yanzu ana yin sa ne a gargajiyance, amma masana sun yi imanin cewa fannin yana da fa'ida mai yawa wanda za a iya amfani da shi tare da saka hannun jari da kuma yin kyakkyawan tsari.
Yawon buɗe ido
Duk da cewa ɓangaren albarkatun ƙasa a Kongo ya fi jan hankali, ba a cika mayar da hankali kan yawon buɗe ido a ƙasar ba.
Ƙasar gida ce ga ɗumbin namun daji waɗanda ake iya gani a wuraren zamansu, waɗanda suka haɗa da gwaggon birai da wasu dabbobi irin su okapi - nau'in dabbar da ba a samu ko ina a duniya.
Sai kuma Virunga, wanda aka kafa a 1925 a matsayin wurin shakatawa na farko a Afirka.
Dazuka masu itace
Kamar yadda shafin worldrainforest.com ya bayyana, DRC ce ke da daji na biyu mai itatuwa mafi girma a duniya.
Dajin ƙasar ya kai kusan kadada miliyan 152.6, wanda ya lashe kaso 67.3 cikin 100 na faɗin ƙasar.
Wannan dajin na ɗauke da halittu da da dama na duniya musamman waɗanda ke barazanar ƙarewa.