Har yanzu ba a gano yawan matsalar da ta afku ba. Hoto / File / Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Ayyukan Yakubu Kasim Yakubu sun tsaya cak, wani ma'aikaci injiniya a kamfanin sadarwa da ke Nijeriya. Lamarin ya faru a farkon wannan watan lokacin da intanet ya dauke gaba daya.

Can a kasar Ghana, Aminu Mohammed ma ya fuskanci irin wannan matsala ta katsewar intanet a banki inda yake aiki a lokacin da babbar matsalar katsewar ta afku.

"A matakin farko ba mu fahimci me yake gudana ba. Mun yi tunanin matsala ce da aka saba gani ta katsewar hanyoyin sadarwa.

"Ana haka ne sai muka yi tunanin wannan babbar matsala ce da ke bukatar kulawa sosai," in ji Aminu yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Awanni bayan haka, hukumar kula da sadarwa ta Ghana ta sanar da cewa matsalar na da girma fiye da yadda ake tsammani. An bayyana cewa wayar da ta hada Yammacin Afirka da Turai a karkashin teku ce ta samu matsala.

Nan da nan sai aka samu labarin wannan matsalar a kasashen Benin, Burkina Faso, Cote d'Ivoire da kuma a can Kudancin Afirka Namibia da Afirka ta Kudu a Kudancin Afirka.

"Kungiyar Ma'aikatan Banki ta Ghana ta fitar da bayani a madadin dukkan bankunan kasar, suna masu tabbatar da cewa ayyukan banki na nan kalau da su. Har yanzu za ku iya samun kudadenku." in ji Aminu.

Wayoyin karkashin teku

Wayoyin da ke karkashin teku na Yammacin Afirka ne suka samu matsala, wayoyin da suka tashi daga yammacin Afirka zuwa Turai, babbar wayar da kuma SAT3.

Mafi yawan wayoyin karkashin teku mallakin kamfanoni msu zaman kansu ne, inda gwamnati take da hannun jari kadan.

A Afirka, masu samar da yanar gizo na dogaro ne kan wayoyin da ke shimfide a karkashin teku da ke bayar da yanar gizo ga masu amfani, in ji Salihu Abubakar, wani kwararre kan Fasahae Sadarwa.

A Nijeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, katsewar yanar gizon ta shafi ayyuka da kasuwaci da dama.

Har yanzu ba a san asarar tattalin arziki da matsalar ta janyo a Nijeriya da sauran yankin ba.

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta bayyana cewa matsalar ta afku ne sakamakon katsewar wayoyin da ke Tekun Sanagal da Cote d'Ivoire.

Babu cikakkun bayanai kan musabbabin afkuwar matsalar, MainOne sun bayyana cewa matsalar wayarsu ta aku a cikin teku a gabar Yammacin Afirka, kuma saboda wata matsala daga waje."

Warware matsalar

A makon da ya tabata, hukumar sadarwa ta Gana ta ce za a dauki tsawon makonni biyar don warware matsalar. Ta ce za a bayar da fifiko ga inda ya fi bayar da matsala, kamar gabar teku da cibiyoyin samar d aruwa da lantarki.

MainOne ya kara da cewa "sun sauya hanya" kuma san samu daidaiton yanar gizon nasu.

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta bayyana cewa an dawo da ayyukan samun data da sakon murya da kaso 90, tana mai ƙarawa da cewar kamfanonin sadarwa sun byar da tabbacin za a warware matsalar.

Duk da an dawo a ayyukan yanar gizon, masu amfani da yanar gizo da dama a kasar na korafin rashin karfin sa.

Riga-kafi

Babbar tambaya a nan ita ce me ya kamata a yi don riga-kafin afkuwar hakan a nan gaba, duba da yadda ba za a iya cewa hakna ba z ta sake afku ba.

Hukmar Sadarwa ta Gana kuma cewa ta yi "Tana bayar da shawarar nasu ruwa da tsaki kan sha'anin kudade da amfani d ahanyoyin sadarwar a gajere, matsakaici da dogon zango don tabbatar da b a samu irin wannan abu a nan gaba ba."

Wasu ƙwararrun na da ra'ayin cewa ya wajaba hukumomi da daidaikun mutane da suka dogara kan yanar gizo su samar da wata hanya daban ta yadda idan ma yanar gizo ya kaste ba za su shiga tasku irin wannan ba.

TRT Afrika