Bayan Ethiopia, Uganda ce kasa ta biyu wajen fitar da gahawa zuwa kasashen waje a Afirka. / Photo: Reuters

Daga Brian Okoth

Kasar Gabashin Afirka ta Uganda na fuskantar rabuwar kai game da Dokar Gahawa ta 2024 da aka yi wa kwaskwarima

Kudirin dokar ya tanadi cewa za a rushe Hukumar Kula da Sarrafa Gahawa ta Uganda (UCDA), wadda ta yi aiki na tsawon shekaru 30, inda za ta zama wani sashe na Ma'aikatar Ayyukan Gona.

Mambobin majalisar dokoki, musamman na jam'iyyun adawa, sun nuna kin amincewa da kudirin dokar, suna cewa rushe UCDA zai jefa makomar samar da gahawa a Uganda cikin hatsari.

Bayan Ethiopia, Uganda ce kasa ta biyu wajen fitar da gahawa zuwa kasashen waje a Afirka

Sashen ya samar da ayyukan yi ga miliyoyin mutane

A 2022, Uganda ta samu kusan dala miliyan 813 daga fitar da gahawa zuwa kasashen waje, inda Ethiopia kuma ta samu dala biliyan 1.5.

Sauran masu samar da gahawa a Afirka su ne Rwanda, Kenya, Tanzania, Ivory Coast da Burundi.

Sashen noma da sarrafa gahawa ya bayar da ayyuka ga mutum miliyan biyar a Uganda, inda sama da gidaje miliyan 1.8 suke noman ta.

Mutanen da kai tsaye - ko ta wata hanya - suke amfana daga masana'antar gahawa a Uganda sun kai kusan mutum miliyan 12, adadi ne da ke nuna irin muhimmancin da gahawa ke da shi ga kasar mai mutane sama da miliyan 45.

'Rikici'

A yanzu, wani kudirin doka na neman a yi kwaskwarima ga hukumar kula da samarwa da fitar da gahawa zuwa kasashen waje. UCDA, a rushe ta, kuma wane bangare a ma'aikatar ayyukan gona ya dinga yin akin da take yi, duk a kokarin rage kudaden da gwamnati ke kashewa.

Karamin Ministan Ayyukan Noma na Uganda, Bright Rwamirama a baya-bayan nan ya fada wa majalisar dokoki cewa a hankali za a rushe UCDA a tsawon shekaru uku, don kauwace wa kawo matsala a fannin.

Rwamirama ya kuma ce batun rushe UCDA ya janyo hayaniya a kasar.

Amma ya ce nan da wani dan lokaci masu ruwa da tsaki za su fahimci cewa gwamnatin da ta mara wa UCDA baya za ta karfafa wa manoma don su samu amfani sosai.

UCDA 'na da muhimmanci' a fannin samar da gahawa

Wani rahoton majalisar dokoki ya ce UCDA na da 'muhimmanci' wajen tabbatar da Uganda a matsayin daya daga kasashen Afirka da ke kan gaba wajen samar da gahawa da fitar da ita kasashen waje.

Kudaden da ake samu da yawa daga masana'antar gahawa na da alaka da kokarin da hukumar ke yi.

Ayyukan UCDA sun hada da tabbatar da ingancin gahawa, bayar da lasisi ga duk masu fitar da gahawa, bai wa gwamnati shawara kan farashin gahawa, tallata gahawar Uganda a duniya da sanya idanu kan masana'antun gahawa, da samar da tsare-tsare a bangaren.

Masu adawa da yin kaskwarima ga dokar UCDA sun ce hukumar na gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, a saboda haka babu dalilin da zai sanya a rushe ta.

Matakin na da manufar 'rage kashe kudade'

'Yan majalisar dokoki na jam'iyyar adawa na cewa rushe UCDA zai janyo matsala game da tantance ingancin gahawa da illata fitar da ita zuwa kasashen waje.

Amma gwamnati, na cewa rushe UCDA zai rage kashe kudade da inganta ayyuka a bangaren samarwa, fitarwa da sarrafa gahawa a kasar.

A shekarar kudi ta Uganda ta 2023/2024, an bai wa UCDA kusan sulai biliyan 65, wanda ya kai kusan dala miliyan 18.

Kudirin neman yin kwaskwarima ga dokar kahwa ta 2024 na gaban kwamitin majalisa, inda 'yan majalisa suke nazari da nazari ga dukkan bangarorin dokar da zummar yi musu kwaskwarima. Matakin zama a gaban kwamitin zai dauki sama da wata guda.

'Gahawa da aka fi so'

A wannan mataki za a iya watsi da kudirin dokar baki daya, ko a matakai uku na nan gama na karatunta a gaban majalisa.

'Yan majalisar dokokin Uganda da dama sun ce suna bukatar neman shawarar jama'arsu kafin daukar wani hukunci kan batun.

Ssewanyana Allan Aloizious, dan majalisa na jam'iyyar adawa mai wakiltar mazabar Makindye ta Yamma ya ce "UCDA na tabbatar da ingancin gahawa a kasuwanni, a Uganda da wajen Uganda. To, idan aka mayar da hukumar ma'aikatar noma, muna da damuwar gahawa din mu da aka fi kauna za a zo a daina kaunar ta."

Shugaban Cocin Anglican a Uganda, Stephen Kazimba ma ya ce cocinsa za ta yi addu'o' na musamman a filin shahidai na tsakiyar Uganda, da ke garin Namugongo, daga 20 zuwa 30 ga Nuwamba don neman "Saka hannun Ubangiji" kan kudirin dokar gahawa, talauci, rikici a cikin gidaje, da ma wasu batutuwa.

TRT Afrika