Abubuwan da kuke bukatar sani kan shan gahawa

Abubuwan da kuke bukatar sani kan shan gahawa

Gahawa wato kofi (coffee) abin sha ne da kusan a kowane sashe na duniya ana amfani da shi.

Za a iya cewa baya ga ruwa da shayi, to shi ne abin sha na uku mafi shahara a tsakanin mutane.

Kama daga nahiyar Turai zuwa nahiyar Amurka da yankin Larabawa da Afirka da Asiya, babu inda ba a shan gahawa.

To amma, me ya sa ake matukar don gahawa haka? Mene ne alfanun shanta ga lafiyar jiki, yaya ya kamata a sha ta?

Tana da wata illa? Akwai wadanda bai kamata su dunga sha ba?

Sannan nau'uka nawa na gahawa ake da su?

Wannan makalar za ta amsa dukkan tambayoyin nan tare da fayyace komai.

Mece ce gahawa?

Wani abin sha ne da ake yin sa daga wani nau'in irin gahawa. Amma sai an kona irin tukunna kafin a sarrafa shi don sha.

Ana dafa shi kamar shayi a sha shi haka, ko kima a saka masa sikari da madara ga mai so.

Dandanon gahawa na da dan daci kuma gahawar na dauke da sinadarin asid da na kafen (caffeine).

Waken Gahawa yayin gasa shi/ AA

A wajen batun launinta kuwa, gahawa kan zo a baka ko ruwan kasa da ya ciza ko ruwan kasa-kasa. Sannan tana da wani kamshi "mai gamsarwa", kamar yadda mafi yawan mutane suka yi ittifaki.

Yaushe aka gano gahawa kuma daga ina?

Duk da cewa a yanzu gahawa ta zama gama-gari a duniya, tarihi ba zai taba manta yadda ta samo asali ba.

Shafin tattara bayanai na intanet na wikipedia ya bayyana cewa tun karni na 15 aka gano irin gahawa a duniya.

A cewar shafin, an fara gano gahawa ne a kasar Yemen inda a can aka fara gasa irin ana sarrafa shi a matsayin abin sha.

Amma a wani kaulin, an ce mutanen kabilar Oromo a yankin Jimma da ke Habasha su ne suka fara gano alfanun gahawa.

Mutanen Yemen kan samo irin ne daga wasu tsaunkuna Habasha da kusa da gabar tekun Somaliya.

Gonar Gahawa a nahiyar a Kudancin Amurka/ AA

Tun daga wancan lokacin kuma sai al'adar shan gahawar ta fara bazuwa zuwa yankin Arewacin Afirka da sauran kasashen Larabawa.

A hankali kuma har aka wayi gari ya shiga yankin Turai ya kuma karasa karade duniya zuwa karni na 20.

Alfanun gahawa ga lafiyar jiki

Binciken masana a fadin duniya ya gano cewa ba don dadin dandano ko kamshi kawai ake shan gahawa ba, don kuwa tana kunshe da sinadaran da ke taimakawa jiki ta hanyoyi daban-daban.

Gahawa/ AA

Mun tattaro alfanu 11 na shan gahawa daga wasu fitattun mujallun lafiya na intanet na Amurka, Healthline da WebMd.

· Kara kuzari da rage gajiya da wartsakar da mutum

· Rage hadarin kamuwa da ciwin siga

· Taimakon lafiyar kwakwalwa da rage hadarin kamuwa da cutar makyarkyata da mantuwa

· Kare hadarin kamuwa da wasu nau’ukan cutar daji kamar kansar hanji da ta mafitsara da ta fatar jiki

· Gyara yanayin ciki da hana mutum narka ƙiba

· Rage yiwuwar kamuwa da cutar damuwa

· Zai iya kare kamuwa da matsalolin da suka shafi hanta

· Inganta lafiyar zuciya

· Yana hana tsufa da wuri

· Kara karsashi musamman ga masu wasannin tsere

· Yawan shan sa na iya jawo tsawon rai – wasu bincke 40 da aka sun nuna cewa shan kofi biyu zuwa hudu na gahawa ka iya rage kamuwa da cututtukan da ke kashe mutane.

Wadanda ya kamata su guji shan gahawa

Duk da cewa masu bincike da dama sun bayyana alfanun shan gahawa ga lafiyar jiki, to sun kuma yi gargadi ga wasu mutane da su guji shan sa da yawa.

Wadannan mutane sun hada da masu ciki da masu shayarwa da yara da masu fama da wasu nau’in cututtuka kamar cutar olsa.

Hadaddiyar gahawa/ AA

Illolin shan gahawa

Sai dai duk da dumbin muhimmancin shan gahawa, likitoci sun yi gargadda cewa a guji shan sa da yawa.

An bayyana cewa duk shan da mutum zai yi kar ya wuce kofi hudu a rana, saboda shan wuce iyaka kan jawo abubuwa kamar haka ga wasu mutanen:

Nau’ukan gahawar kasashen Afirka da dandanonsu masu dadi

Nahiyar Afirka na daya daga cikin wadanda suka fi samar da gahawa a duniya.

Kasashen nahiyar da yawa musamman na gabashi na samar da gahawar da ke taimaka wa habakar tattalin arzikinsu.

Akwai kasashe hudu na nahiyar da suka fi kowa samar da gahawa, da ya kamata ku san su, wato Habasha da Kenya da ke kan gaba, sai Burundi da kuma Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

Gahawar Habasha

Habasha

Samar da gahawa ta fara a Habasha kimanin shekara dubu 1,100 da suka gabata, ta ci gaba har zuwa yau a “mataki na uku” – inda kasuwancinta ke jan hankalin matasa ta yadda suke bude wajen shan ta a kusan ko ina.

Gawahar kasar Habasha na da dandano da kamshi na musamman --- sannan an san yadda irin gahawa na Yirgacheffe yake da dandanon zaki da ke daidaita jiki da asid.

Irin Yirgacheffe na da kamshin kayan kamshi kuma ana bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowanne a Afirka --- kuma shi ne na takwas mafi karbuwa a duniya.

Kwayoyin waken gahawa kafin su bushe/ AA

Kenya

Duk da a makare aka fara noman gahawa a Kenya, kasar ita ce ta biyu a Afirka wajen samar da gahawa samfurin Arabica, bayan makwabciyarta Habasha.

Gahawar Kenya ta ‘African Arabica’ ba wai ta zama daya daga cikin shahararrun gahawa ba ne, don kuwa ita ce ta 10 mafi karbuwa a duniya.

An san ta da dandanonta mai malalowa da kuma kamshi na musamman.

Gonar gahawa a Kenya/ AA

Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo

Ana fitar da irin gahawa mafi shara a Kongo daga kungiyar manoman gahawa ta Virunga, wata kungiya ce da manoma suka kafa a yankin Kivudake da ke gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

Wannan iri na gahawa na da dandano na daban: suna da dandanon zaki da na kayan marmari, wanda kuma wani kamshi mai ratsa zukata ke biye musu.

Gonar gahawa a Jamhuriyar Dimikradiyyar Kongo/ AA

Burundi

Manyan abubuwan da Burundi ta fi fitarwa su ne gahawa da ganyen shayi, wanda shi ne ke kawo mata kashi 90 cikin 100 na kudaden kasashen waje ga kasar.

Gahawar AA Kirimiro Burundi na da karfi da kuma wadatarwa, tana da dandanon lemon tsami da nau’in bakin shayi, ga kuma dan kamshin kayan kamshi - dukkan su na tattare da kamshi na musamman.

Bayanai daga: Kungiyar Manoma da Masu shan gahawa ta Afirka

TRT Afrika