Daga Sylvia Chebet
Kamar gidajen adana kayan tarihi, manyan biranen duniya na tattare da tarihi, al'adu, dabi'u, da zamantakewar dan adam, har ma a lokacin da suke habaka.
Babban birnin Morocco, Rabat, ya zama abin misali da mallakar dukkan abubuwan da marubuta suke nema a wani gari - hanyoyi, layuka, gine-gine, da dandalin jama'a da dama na da labaran da suke jiran a yada su.
Kamar yadda marubucin Morocco Tahar Ben Jelloun ya bayyana "Rabat waje ne da gargajiyanci ya hade da zamani, da kuma adabi ne gadar da ke tsakanin biyun."
Jelloun ya bayyana mai gaskiya a lokacin da darakta janar na UNESCO, Audrey Azoulay, ya sanar a wannan watan cewa Rabat ya zama "Babban Birnin Litattafai na 2026".
Tun 2001, Rbat ne birni na 26 da ya samu wannan babban matsayi, ina ya karbi kambin daga birnin Rio de Janeiro na Barazil.
Shi ne birni a Afirka na shida d aya samu wannan karramawa bayan Alexandria na Masar a 2002, Fatakwal na Nijeriya a 2014, Conakry babban birnin Guinea a 2017, da babban birnin Gana Accra a 2023.
"Zama Babban Birnin Litattafai na Duniya babbar nasara ce ga malaman adabi na Rabat," in ji daraktar kula da litattafai, dakunan karatu da kundin bayanai ta Morocco Latifa Moftaqir, yayin da take tattaunawa da TRT Afrika.
"Wannan girmamawa ta sanya birnin zama a kan gaba a taswirar duniya kuma zai karfafi gwiwar abokan aiki a nahiyar. Yana kuma nuna cewa Afirka na samun shuhura saboda gudunmowar da nahiyar ke bayarwa ga adabi a duniya."
A yayin da suke daukar wannan mataki, Kwamitin Babban Birnin Litattafai na UNESCO ya kalli dombin tarihin dake birnin, adana kayan al'adu da gargaji da kayatarwar sa.
Chakuduwar tsoho da sabo
Hassan Najmi, tsohon shugaban Kungiyar Marubuta ta Morocco kuma marubucin litattafai biyu na kagaggen labari da wake da aka fassara zuwa sama da yaruka goma, ya ira sunan gainsu na Rabat da "birnin haske".
Ya fada wa TRT Afrika cewa "gari ne mai tsafta da girma da ke kunshe da jami'o''i da masu kaifin basira.
An kafa Rabat a karni na 12, na nan a gabar tekun Atlantika a arewa maso-yammacin Morocco. UNESCO ta bayyana birnin a matsayin mai tsarin gini da babu irin sa, wanda ya hada fasahar Musulmai Larabawa na dauri da zamanincin da ya zo daga Yammacin Duniya.