Ana sarrafa rogo tare da cin ta hanyoyi daban-daban a fadin Afirka. Hoto: Reuters  

Daga Firmain Eric Mbadinga

Shekaru da dama bayan fara shigarsa Afirka daga yankuna masu zafi na Amurka, wani abin mamaki shi ne yadda Rogo ya shiga cikin nau'in abincin gargajiya na al'ummomi a yawancin sassan nahiyar.

Ma'aikaciyar gidan abinci Éliane Obiyi, 'yar asalin lardin Haut-Ogooué ta Gabon, tana cikin miliyoyin 'yan Afirka da suka haɗa rogo a cikin kusan kowane irin abincin da take sayarwa.

A matsayinta na wadda ta samu horo a fannin kiwon lafiya, ta kasance mai matukar mayar da hankali kan abubuwan da take amfani wajen hada abincinta, kuma rogo na daga cikin nau'in abincin da ke cikin wannan lissafi.

Ana markada rogo a cikin inji ya zama gari. Hoto: TRT Afrika

"Daga cikin nau'o'in albarkatun noma da na fi son amfani da su, rogo na kan gaba saboda ana iya sarrafa shi ta hanyoyi daban-daban, kuma yana da matukar muhimmanci ga al'adunmu na Afirka," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Éliane ta soma kasuwancinta na dafa abinci ta hanyar siyarwa a bakin titi. Daga baya ta koma siyar da abincin daga gida kafin buɗe gidan abincinta a Franceville, babban birnin lardin Haut-Ogooué.

A cikin duk waɗannan matakai da ta bi na kasuwancinta, iya sarrafa nau'in abinci na rogo na daga cikin dabarun da ta koya daga wajen iyayenta.

Ta ci gaba da sabunta waɗannan hanyoyi da ta koya inda ta yi ta fitar da wasu sabbin ire-iren abinci da rogo a matsayin sinadarin farko.

“Ana hada Dokô ko obamba ta hanyar jiƙa rogo mai ɗaci a cikin ruwa mai yawa na tsawon wasu kwanaki don a tausasa shi,” in ji Éliane.

Rogo da aka sarrafa /  Hoto: TRT Afrika

“Daga nan kuma sai a tace shi, a nika shi cikin injina har sai an sai ya yi kauri da kuma laushi. bayan haka, sai a daura shi kusa da wuta ya ɗan tafasa, mataki na karshe shi ne a nade wannan hadin cikin takardar gargajiya sannan a gasa shi na tsawon kusan mintoci 20."

Girke- girge iri daban-daban

Baya ga nau'in rogo ake kira Dokô wanda ake ci a fadin Gabon da sauran ƙasashe Afirka kamar Kamaru, da Guinea da DR Congo da Jamhuriyar Kongo da kuma Angola, Attiéké wani nau'in abinci ne da ake hada wa rogo.

''Idan za a sarrafa Attieke, dole ne sai samu sabon rogon da aka ciro shi daga kasa sannan a wanke, a marƙada shi a cikin Inji. Da zarar ya nuƙu sai a matse kashi 90 cikin 100 na ruwansa. Bayan wannan matakin sai a dafa gindin rogon a rana guda,'' in ji Éliane.

"Ka'idar ita ce a ci gaba da motsa shi a kan wuta kadan don hana shi mannewa a cikin tukunya, sannan sai a busar da shi a cikin wata tukunya mai dauke da ruwa har na tsawon mintuna kimanin biyar."

Wata hanya ta daban da ake sarrafa Rogo wadda har ganyensa ma ana ci, shi ne Gari. Ana sarrafa shi kamar yadda ake hada Attiéké sai dai abu daya ne kawai ya banbantasu.

Éliane Obiyi kwararriyar ma'aikacin kiwon lafiya ce. Hoto: TRT Afrika.

"Bambanci da ke tsakanin yadda ake sarrafa Gari da Attiéké na zuwa ne bayan an tace ruwan jikin rogon, dukka nau'in abincin ana nika su ne a Inji sannan a tace su.

Sai dai Attiéké ana dafa shi ne zarar an gama tace shi, shi kuma Gari ana busar da shi a rana na tsawon wasu kwanaki" in ji Éliane.

Ana yawan cin Gari a matsayin hatsi tare da madara da sukari ko kuma a dafa shi da ruwa da mai tare da ɗan gishiri kaɗan.

Wani manomin rogo a Yamoussoukro babban birnin kasar Cote d'Ivoire. Hoto: Reuters

Kamar yadda Attiéké da Dokô da kuma Gari suka yi farin jini musamman a yankin Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka, shi ma Foufou ya samu karbuwa sosai.

Wannan nau'in abincin da ake kira da Fufu, ana yin shi ta hanyar tafasa garin rogo kuma galibi ana cinsa da miya.

A matsayinta na mai dafa abinci iri daban-daban , Éliane ta ce ta lura da yadda kwastamominta suka fi sha'awar Dokô don haka tafi maida hankali wajen hada shi sosai.

"Har yanzu ina da karin ilimi da nake bukata, amma wannan kasuwancin yana da fa'ida sosai kuma a ƙarshe zai ba ni damar zama mai cin gashin kaina ta hanyar samun kuɗi." in ji ta.

A mataki na gaba cikin kasuwancinta, wanda ya ƙunshi ayyukan hada abinci iri-iri, Éliane na burin mayar da gidan dafa abincinta da ire-iren nau'in abincin da ake hada wa da rogo inda take sanya idonta a Libreville, babban birnin Gabon, inda aka fi buƙatar nau'in abincin rogo daban-daban.

Farashin rogo a Gabon ya tashi daga kudin Cefa 500 zuwa sama a kan ko wane Gram 500. Kazalika farashin ya shafi Foufou da Gari da kuma ganyen rogo, wadanda ake amfani da su a matsayin kayan lambu.

TRT Afrika