Kaunar da Jean-Luc ke yi wa kwallon kwando ce ta kai shi ga smaun akrfin gwiwar talafawa wasu a fannin wasan. Hoto: Jean-Luc

Daga Firmain Eric Mbadinga

A matsayinsa na mutumin da ya girma a Paris, Jean-Luc Agboyibo ya fara kwallon kwando da kafar dama. Ya kware a harkokin wasan, inda ya samu nasibin da ya wuce na farin cikin wasan na kwallon kwando.

Bayan wasu shekaru ne Lean-Luc ya fahimci yadda kaunarsa ga kwallon kwando za ta kai shi ga samun karfin gwiwar tallafa wa wasu a fannin wasan.

A 2012, matashin ya kafa kungiyar Matasa Masu Jan Ragama Domin Wasanni da Ci-gaba, kungiyar da ke amfani da wasanni, musamman kwallon kwando, a matsayin wani jigon koyarwa da ci-gaban rayuwar maza da mata a tsakanin kabilarsa da ke Togo da Cote d'Ivoire.

Shirin da kungiyar ke gabatarwa na Miledou, na hada kai da gasar NBA, don smaun damar mika kwararrun matasan Afirka ga kungiyoyi daban-daban.

Jean-Luc ya shaida wa TRT Afirka cewa "A wajen wani taro a 2012 ne aka kafa Miledou tare da Amadou Gallo da John Manyo Plange, tsohon daraktan NBA a Afirka, wanda tuni ya karbe ragamar jagorancin Gasar Kwallon Kwando ta Afirka."

"A lokacin ina dab da kammala karatuna a Faransa, sai na ji ina bukatar bayar da gudunmawa ga kyautatuwar rayuwar matasan Togo ta hanyar kwallon kwando. Ba su yi tsammanin za su yi aiki tare da NBA ba, sai kawai na yanke shawarar kulla alaka da su."

Kungiyar Jean-Luc ta Meledou na hada kai da NBA don trainon 'yan wasan kwallon kwando. Hoto: Jean-Luc

Nasara a rayuwa

Bayan shekaru sama da goma, kwarin gwiwar Jean-Luc Agboyibo da karsashinsa na horar da matasa a Afirka ta hanyar wasanni, musamman ma kwallon kwando, sun zama abin da ba za a iya mantawa da su ba.

Miledou na samar da damarmaki da dama ga matasan da aka kama aka daure saboda aikata wani babban laifi, wani da yake fuskantar matsala a yanayin zamantakewa, ko wani matashi dan tawaye da yake shan wahala a harkokin karatu, inda suke sake gina sabuwar rayuwa.

A cibiyar Miledou da ke Kouve, a yankin Togo da ke da teku, Jean-Luc da mambobin kungiyarsa na aiki ba gajiyawa don fadada isar su ga jama'a, daga koyar da kwallon kwando zuwa ga taimakon bayar da ilimi da kyautatuwar zamantakewa.

"Ina son samar da yanayin da matasan kasata za su samu damar da za ta daukaka su," in ji Jean-Luc, wanda yana daya daga cikin "Jagorori matasa na Afirka 100" da Asusun Faransa-Afirka ya fitar a 2021."

Jean-Luc da mambobin kungiyarsa na aiki ba gajiyawa don isa ga al'umma sosai. Hoto: Jean-Luc

Mutum mai manufa

Ba kamar sauran matasan Togo ba, Jean-Luc ya yi rayuwa cikin farin ciki a Paris, tare da ingantacciyar ruwa da ilimin zamani. Ya zauna tare da 'yan'uwansa mata inda iyayensu kuma suke zaune a Togo.

Bayan kammala digirin farko a bangaren sha'anin kudi da tallata haja a jami'ar Paris-I-Panthéon-Sorbonne da kuma digiri na biyu a bangaren kula da wasanni daga Makarantar Wasanni ta Amos, Juan-Luc ya yi mu'amala da kwararru kan yadda zai cim ma burin da yake da shi a rayuwa.

A 2014, shekara biyu bayan fara aikin Cibiyar Kouve, Jean-Luc ya fara harkokin wasan kwallon kwando da zuba jarin CFA miliyan 5. "A ranar kaddamar da shirin, mutane sun tunkare mu suna tambayar me ya sa ba mu saka wadannan kudade a wani wajen da ya fi wannan muhimmanci ba," in ji shi.

Tare da jajircewa, madalla ga wayar da kan mutane da gasa da aka halarta a lokuta daban-daban, Miledou ya ja ra'ayin jama'a matasa a Togo da Cote D'Ivoire wajen amincewa da manufofin Jean-Luc.

Shirin Miledou na taimaka wa yara mata da ke karatu kuma iyayen su a su da hali sosai. Hoto: Jean-Luc

A 2017, Jean-Luc ya samu izinin kaddamar da shirin Miledou a gidan gyaran hali na MACA da ke babban birnin Abidjan. Manufar ita ce a samar da sabuwar rayuwa ga fursunoni matasa da ke da kaifin kwakwalwa.

Jean-Luc ya kuma dauki nauyin karatun yara mata da iyayensu ba su da hali. Da yawa daga wadannan yara mata sun dakatar da karatuttukansu saboda juna biyu.

"A 'yan shekarun farko, mun dogara kan neman taimako daga jama'a. Bayan shekara ta uku, sai kungiyoyi da masu bayar da tallafin kudi suka fara fahimtar mu."

A yayin da manufarmu ba ta zama ta wasanni kawai ba, mun samu damar jan hankalin kungiyoyin tallafawa ilimi, shigar da mata makarantu da tallafa musu a zamantakewa. Daga shekara ta biyar zuwa sama, mun tara kudade sosai."

Babban ci-gaban da Miledou suka samu ya hada da hadin gwiwa da Cibiyar Obama da kuma Tarayyar Kwallon KWando ta Afirka a 2019.

Shirin Miledou na gabatar da sabuwar rayuwa ga matasa. Hoto: Jean-Luc

Mataki mai tsauri

Jean-Luc ya ce a lokacin da damar haduwa da BAL ta zo, ba shi da tabbacin ko za su amfanar da Miledou.

"Duk da na sa irin yunkuri da damar da kungiyata ke da shi Ina da babbar tambaya game da tsarin kasuwancinmu da yadda ayyukan mu za su dore," in ji shi. "A lokaci guda, dama ce mai kyau a dinga samun horo a kungiyar da ke aiki da NBA."

Jean-Luc ya rike mukamai daban-daban tare da BAL tun daga 2020 har zuwa watan Agustan 2023. A watan Satumba, ya zama shugaban sashen Omega Sports Holding, wani kamfanin zuba jari da ya mayar da hankali kan kashe kudade a harkokin wasanni a Afirka.

Miledou na da cikakkun ma'aikata bakwai da masu bayar da shawara uku da kuma malamai 40 da ke ayyuka a yankuna 12 na Togo da Ivory Coast.

A watan Nuwamban 2023 Jean-Luc ya halarci babban taron 'Le Monde Afrique' a Abidjan. / Hoto: TRT Afrika

Baya ga bangaren kwallon kwando, matasa da dama da aka baiwa horo a karkashin Miledou sun samu nasara a wasu bangarori. Wasu na aiki a bangaren kere-kere wasu a manyan kamfanoni irin su Microsoft.

Wannan babban yunkuri na Jean-Luc na ci-gaba da an hankali da kuma karfafa gwiwa, da ilhamar da suke samu daga falsafar Nelson mandela da ke cewa "Wasa na da karfin sauya duniya. Na da karfin hada kan mutane da karfafa musu gwiwa."

TRT Afrika