Duma Boko ya yi yakin neman zabe a karkashin jam'iyyar adawa ta BNF. Photo/Duma Gideon Boko X

Daga Firmain Eric Mbadinga

Ba a cika samun mika mulki cikin ruwan sanyi ba, kuma musamman yadda aka samu sauyin hannu bayan kusan shekaru sittin na mulkin jam'iyya guda a kasar da ke da mutane miliyan 2.3 da suka yi zabe don samun sabuwar rayuwa.

Bostwana ta zabi zama ta musamman mai ban mamaki a lokacin zaben shugaban kasa na 30 ga Oktoba inda suka zabi Duma Gedeon Boko na jam'iyyar BNF inda ya zama shugaban kasar na shida kuma na farko da ba daga jam'iyyar BDP ba.

Idan sanarwar nasarar dan adawa ba tare da wani rikicin siyasa ba, kuma abinda ya fi bayar da mamaki shi ne yadda shugaba mai barin gado Mokgweetsi Masisi, ya amince da shan kaye tun ma kafin a sanar da sakamakon zabe a ranar 1 ga Nuwamba.

An samar da BNF a 1965, shekara guda kafin kasar ta samu 'yancin kai, kuma BDP ta yi mulki na tsawon shekaru 58.

A wajen bikin mika mulki a ranar 4 ga Nuwamba, yadda Masisi ya marabci mai maye gurbinsa ya cika alkawarin da ya yi.

"Na san ina da alhakin tabbatar da mun samar da tsayayyen tsari saboda ba mu taba sauya gwamnati ba, kamar yadda sauran jam'iyyu ke karba-karba a sauran kasashe," in ji shugaban mai barin gado. "To babban nauyin a kaina yake, dole ne na yi jagoranci abin koyi."

Abin koyi a nahiyar

A wajen masu sanya idanu da dama, wannan al'amari na Bostwana na samar da yanayin da sauran kasashen Afirka za su yi koyi.

An yaba wa Bostwana saboda gudanar da mika mulki ga sabuwar gwamnati lami lafiya.  Photo/Duma Gideon Boko X

"Wannan ya karfafa gwiwar tsarin dimokuradiyya, wanda za a iya gani a zaman lafiyar kasar," Nicholas Dominique, wani kwararre a sha'anin tsaro da siyasar kasa da kasa ya shaida wa TRT Afrika.

"Akwai girmama cibiyoyi da dokoki a kasar, duk da cewa jam'iyyar da ke mulki na iya amfani da hanyoyin da suka saba doka don ci gaba da zama a kan mulki. Sabanin hakan kuma, sai suka karbi tsarin dimokuradiyya, kuma aka baiwa hukumar zabe ta yi aiki ba tsare da wata matsala ba."

Daga Seretse Khama, shugaban kasar Bostawa na farko, zuwa ga Masisi, tsohon shugaban kasar wanda ya fito daga BDP.

A yayin da Boko ya hau mulki a yanzu, ba kima da hoton BNF kawai ne abin kalla ba a matsayin ta na jam'iyyar dimokuradiyya ta 'na socialist. Taken BNF shi ne "Chanji ya zo", sakon da ya sanya fata nagari da tsammanin kawo babban sauyi a kasar.

Sanannun zabi

Bukatar neman sabon salo da tsari na ga yadda kasa ta girmama a siyasance, musamman a irin kasar da ke son zama mai matsakaiciyar damar tattalin arziki. A yanzu, kashi 88.5 na jama'ar kasar na iya rubutu da karatu.

"Bostawana na karfafa shigar 'yan kasa siyasa ta hanyar bayar da damar jefa kuri'u da wayar da kan 'yan kasa. A ra'ayina, fitar 'yan kasa jefa kuri'a sosai na kara tabbatar da halascin sakamakon zabe." in ji Dr Dominique.

"A tarihi, jam'iyya mai mulki ce ke lashe dukkan zabukan baya, amma a cikin lokaci, sai 'yan adawa suka samu karfin gwiwar nuna tirjiya."

Yadda aka mika mulki ba tare da wata matsala ba a Bostwana na ci gaba da janyo kace na ce a duniya, kuma musamman ma a kasar da ta dinga yawan fuskantar rikicin siyasa.

"Mun yada da shugabanci abin koyi na shugaban Bostwana mai barin gado, Mokgweetsi Keabetswe Masisi, wanda ya amince da sakamakon zaben da aka yi, yana mai shaida karfi da ikon tsarin dimokuradiyya a Bostwana," in ji Shugaban Kasar Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi, a sakon taya murna da ya taya Boko.

Kungiyar Cigaban Kasashen Kudancin Afrika ma ta aike da sakon taya murna inda ta shaida an gudanar da zabe lami lafiya.

Al'adar danniya

Kasashen da ba su da sauyin dimokuradiyya, irin su Bostwana, har zuwa baya-bayan nan na da yawa a Afirka. Kasashe da dama na karkashin shugabancin jam'iyyun da suke kan mulki tsawon shekaru.

A Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC ta rasa nasarar zabe a karon farko tun bayan kawar da mulkin tsiraru farar fata.

Kayar da BDP kamar kayen da ANC ta sha ne, kuma na nuni da yadda masu jefa kuri'a a Afirka ke barin ra'ayin rikau da tsauri a yayin jefa kuri'a.

Masisi na Botswana ya taya murna ga Boko bayan jam'iyyarsa ta sha kaye a babban zaben 30 ga Oktoba. Photo: Reuters

"Jama'ar kasar sun amince da kawancen kawo sauyin dimokuradiyya , musamman ma a tsakanin matasa, wadanda aka yi wa alkawarin samar da tsarin tattalin arziki mai kyau da kara mafi karancin albashi." in ji Cheikc Tourad Traore na Hukumar Tallafi ta Amurka USAID da ke Dakar.

Dr Dominique na da ra'ayin cewa sauyin siyasa a kasashe na da muhimmanci wajen samun gudanarwa na walwalar jama'a. Tsakiyar Afirka na daya daga wadannan yankuna.

"Kasashen da ke zuwa zukatan mutane su ne Kamaru, Equatorial Guinea da Congo Brazzaville, wadanda dukkan su na iya samun ilhama daga Bostwana, Uganda da Togo ma haka."

Idan aka kalli batun ta bangaren jin dadin zamantakewa da walwalar tattalin arziki, hasashen na da sanya fata nagari.

"A wasu yankunan irin su Yammacin Afirka, inda sojoji suka kifar da gwamnatoci ta hanyar juyin mulki don sauya salon siyasa, hakan na da muhimmanci ga yadda jama'a suka aminta, ciki har da kungiyoyin kwadago da matasa, bangarori biyu da suka bayar da gudunmowa sosai ga nasarar UDC." in ji Dr Dominique.

Traore ya yi amanna cewa ya rage na jam'iyyu su mayar da takubba kufe a yayin dabbaka akidun dimokuradiyya.

Ya fada wa TRT Afrika cewa "A lokacin ake girmama lokutan gudanar da zabe, ana yin takara cikin adalci, kamar yadda ake gani a Bostwana, muna karin ganin yadda mutane za su yi kokarin zabi mai kyau bayan samun bayani."

TRT Afrika