Daga Mazhun Idris
An yi al'ajabin ganin totocin Rasha a hannun wasu masu zanga-zangar kan hauhawar farashi a Nijeriya. Lamarin ya haifar da zarge-zarge, abin da masu sharhi suke kallo a matsayin abin damuwa.
Zanga-zangar, wadda matasa suka jagoranta ta fara ne a ranar 1 ga Agustan a kasar ta Afirka ta Yamma, inda suke bayyana halin da kasar take ciki ta kunci da tsadar rayuwa tun bayan janye tallafin man fetur a bara, ta jawo hankalin mutane a lokacin da aka fara ganin ana ta daga tutar Rasha a wuraren zanga-zangar da dama.
Don haka, mece ce alakar Rasha da damuwar mutanen Nijeriya a kan kuncin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro?
A daidai lokacin da wasu suke ganin kawai matasan ne suke bayyana adawarsu da tsoma bakin kasashen Yamma a harkokin kasarsu, wasu kuma suna da fahimtar cewa watakila akwai lauje cikin nadi daga 'yan aiken Rasha domin yada farfaganda.
Amma ko ma mene ne, masana suna ganin lallai akwai matsaloli jibge a tattare da tattalin arzikin Nijeriya, da ba ta bukatar taimakon Rasha.
"A bayyana yake cewa lallai mutane sun fusata saboda wasu matakai da aka aro daga kasashen Yamma kamar janye tallafin man fetur da barin Naira ta kwaci kanta a kasuwa kamar yadda Bankin Lamuni da Bankin Duniya suke ba kasar shawara," inji Hassan L. Abubakar, masanin halayyar dan Adam a Jami'ar Jihar Kaduna a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Barista Sani Gwale daga Jihar Kano, inda aka gani ana daga tutar ta Rasha sama da sauran wuraren, ya ce watakila wasu daga cikin masu zanga-zanga suna ganin daga tutar na cikin hakkin bayyana ra'ayinsu.
Matsalar ita ce dole gwamnati za ta dubi lamarin a matsayin karya dokar tuta da tambarin Nijeriya wato Nigeria Flag and Coat of Arms Act.
Ko da yake taken zanga-zanga shi ne kawo karshen mulki mara kyau, abin da yake kan gaba wajen jawo zanga-zangar shi ne janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi, wanda ya jawo hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
A wasu jihohi, zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma, inda aka rasa rayuka, sannan aka barnata dukiyoyi da kadarorin mutane da na gwamnati.
Martanin gwamnati
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar da su zo a tattauna, sannan kuma da wani matakin da yake kama da yunkurin dakile masu daga tutar ta bayan fage.
A ranar 5 ga Agusta, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Nijeriya wato DSS ta fitar da sanarwar kama wasu teloli a Kano wadanda ake zargi da dinkawa tare da rarraba tutar ga masu zanga-zangar.
Ita ma Rundunar 'Yan sanda ta ce ta kama gomman mutane da ake zargi da daga tutar Rasha.
Ita ma Rundunar Tsaro ta yi Allah wadai da daga tutar, inda suka bayyana hakan da cewa, "ana sa yara suna cin amanar kasa."
A nata bangaren, Ofishin Jakadancin Rasha a Nijeriya ta nesanta kanta da "amfani da tutarta a zanga-zangar."
Domin nanata cewa ba ta da hannu a al'amuran da suka shafi Nijeriya, Ofishin Jakadancin ya wallafa a shafinsa na intanet cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar da kansu suka yanke shawarar daga tutar Rasha din, ba tare da sa hannun wata hukumar Rasha ba.
Hanyar daga hankali
Chiroma Hantsi, wani mazaunin Abuja ya ce tun kafin a fara zanga-zangar ya ji wasu matasa suna cewa za su daga tutar Rasha tare da kiran sunan Vladimir Putin.
"Sun ce idan har ana so zanga-zangar ta jawo hankalin kasashen duniya, dole su yi shigen abun da aka yi a Jamhuriyar Nijar," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.
An ga irin hakan Kaduna da Kano, jihohin da su ne cibiyar Arewa, inda matasa suka rika daga tutar ta Rasha. An ga bidiyoyi a kafafen sadarwa na wasu teloli suna ta dinka tutar ta Rasha.
Masu bibiyan al'amura suna nuna ra'ayoyi mabambanta a kan dalilin da ya sa matasan suka yi haka. A zanga-zangar #EndSARS da aka yi a 2020 a kan adawa da zaluncin 'yan sanda, tutar Nijeriya kawai aka rika dagewa.
Adawa da kasashen Yamma
Abubakar ya ce yana ganin daga tutar Rasha din na da alaka da kiyayya da kasashen Yamma da ke karuwa a tsakanin kasashen Afirka ta Yamma.
"Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna kallon Rasha a matsayin kasar da za ta iya cetonsu," in ji shi.
"Sai dai kamar kasashen Yamman, ita ma Rasha ribarta ce a gabanta."
A Mayu, wasu kungiyoyin fararen hula suka gargadi Gwamnatin Nijeriya a kan rade-radin da ake yi cewa za ta shiga wata yarjejeniyar soja da Faransa da Amurka, wadda za ta ba da dama a dawowa da sojojin da aka kora daga kasashen yankin Sahel zuwa Nijeriya.
Wasikar ta samu sa hannun wasu kungiyoyi ne ciki har da wata wadda tsohuwar Shugabar Hukumar INEC ta sa hannu. Kungiyoyin sun gargadi Shugaba Tinubu da Majalisar Dokoki da kada su bari sojijin kasashen Yamma su dira a kasar.
A matsayin kasar da Biryaniya ta raina, ana ganin Nijeriya na da alakar diflomasiyya da kasuwanci mai kyau da Biryaniya da Amurka da Faransa.
Ratsa kasashen yankin Sahel
Duk da cewa 'yan Nijeriya da dama suna fargabar sanya hannun Faransa a harkokin cikin gidanta, Rashar tana kara samun karbuwa a yankin na Sahel.
Bayan juyun mulkin da aka yi a Nijar da Burkina Faso da Mali da Guinea, wasu sun yi farin ciki da juyin mulkin a matsayin samun 'yanci daga Faransa da mulkin mallakar kasashen Yamma gomman shekaru bayan samun 'yanci.
Kasashen na yankin Sahel sun samu tallafin soji da na inganta tattalin arziki daga Rasha, wanda hakan ya sa suka yanke alaka da Faransa da Amurka, sannan suka fatattaki sojojin Yamma daga kasashensu.
Kasancewar sojojin Rasha a kasar da ke makwabtaka da Nijeriya na cikin dalilan da suka sa Abubakar yake tunanin sun jefa wasu 'yan Nijeriya cikin rudu a game da daga tutar ta Rasha.
Nijeriya ta dade tana fama da rikice-rikice, ciki har da rikicin Boko Haram da ya kai shekara 20. Wannan ne ya sa masu sharhi ba za su yi mamaki ba idan aka ce Rasha na da hannu a rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin na Arewa.
Wata fahimtar ita ce Kungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasashen Afirka ta Yamma, wadda Shugaba Tinubu ke jagoranta, ana ganin kimarta ta ragu sosai bayan da ta janye barazanar da ta yi afkawa kasar Nijar domin dawo da zababben Shugaban Kasar bayan juyin mulkin Yulin 2023.
A yanzu da manyan kasashen masu karfin ikon suke kara nuna isa, babbar manufar ita ce yaki da kuma kokarin fatattakar kasashen Yamma daga Afirka.
Wata alamar da ke kara nuna cewa Afirka ta kawo karfi shi ne yadda wasu karin kasashen Afirka guda biyu suka shiga Kungiyar BRICS wato Habasha da Masar. Wannan lamarin ya faru ne kuma daidai lokacin da kungiyar ke karkashin jagoracin kasar Rasha.