Yanzu haka Afirka ta Kudu na sa ran fitar da kwalan iri na lemun Valencia miliyan 51.6 mai nauyin kilogiram 15, Hoto: AA    

Afirka ta Kudu ta yanke adadin hasashenta na fitar da 'ya'yan lemu a kakar noma ta shekarar 2024 sakamakon tsananin yanayi da yankuna masu noman lemu a ƙasar suke fuskanta, a cewar ƙungiyar masu noma 'ya'yan itatuwa dangin lemu a ƙasar a ranar Laraba.

Sanarwar ƙungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kayan lemu a duniya ke ƙara hauhawa.

Kazalila hasashen Afirka ta Kudu ya zo daidai da Brazil wadda ke kan gaba wajen samarwa da kuma fitar da lemu zuwa kasashen duniya ta tsinci kanta a mafi munin yanayi bayan shekaru 30 da suka wuce sakamakon rashin kyawun yanayi da kuma cutar lemu da ake fama ita, lamarin da ya sa farashin ya ƙara hawa sosai.

Afirka ta Kudu ita ce kasa ta biyu a duniya wejen fitar da 'ya'yan itacen lemu baya ga Masar, sannan baki ɗaya ita ce ta biyu wajen fitar da 'ya'yan dangin lemu a duniya bayan Sifaniya.

Ƙasar tana fitar da mafi yawan 'ya'yan itacen ne zuwa ƙasashen Turai da yankin Gabas ta Tsakiya da Kudu maso Gabashin Asiya da Arewacin Amurka da kuma Birtaniya da Rasha.

Yawan kayayyakin da take fitarwa

A sanarwar da ƙungiyar masu noman 'ya'yan itacen dangin lemu ta Afirka ta Kudu (CGA) ta fitar, ta ce ta yanke adadin hasashen samar da 'ya'yan itacen ne sakamakon guguwa da ambaliyar ruwa a Citrusdal da ke yammacin birnin Cape da kuma yanayin sanyi a Marble Hall da Grpblersdal a Limpopo.

A halin yanzu dai Afirka ta Kudu na sa ran fitar da kwalayen iri na lemun Valencia miliyan 51.6 mai nauyin kilogiram 15, adadin da ke kasa da hasashen da aka yi a yayin buɗe noman kakar bana kan miliyan 58, in ji CGA.

A shekarar 2023 Afirka ta Kudu ta fitar da kwalaye iri na lemun Valencia miliyan 52.21.

Kazalika ƙasar na san ran fitar da 'ya'yan iri na lemun Navel miliyan 21 mai nauyin kilogram 15 a cikin wannan shekarar, adadin ƙiyasin farko na kwali miliyan 25.7 da aka yi a baya.

Ƙasar ta fitar da kwali miliyan 24.8 zuwa ƙasashen waje a bara.

''A bayyane take cewa yanzu ba za a samu yawan kayan lemu a wannan kakar ba. Muna duba yanayin daidaito na kasuwa,'' in ji sanawar da Jan- Loius Pretorious, mataimakin shugaban ƙungiyar CGA kuma mai noman lemu a Limpopo ya bayyana.

AFP