Nijeriya ta sanar da za ta dinga bayar da lasisin hakar ma'adanai ga kamfanonin da za su sarrafa su a cikin kasar kawai, in ji kakakin gwamnati a ranar Alhamis.
Wannan na nufin an samu sauyi daga tsohon tsarin da Nijeriya ke kai na fitar da danyen albarkaun kasa, a lokacin da gwamnatocin kasashen Afirka ke kokarin amfana da albarkatun kasashensu.
Domin habaka zuba jari, Nijeriya za ta dinga karfafa gwiwar masu zuba jari ta hanoyi da suka hada da janye haraji ga kayan hakar ma'adanai da aka shigo da su, saukakan hanyoyin samar da makamashin lantarki, bayar da damar tafiya da arzikin da aka samu a kasar tare da karfafa tsaro, in ji Segun Tomori, kakakin MInistan cigaban albarkatun kasa.
"A madadin haka, dole ya sanya idanu mu sake nazari kan shirin da kamfanonin kasashen waje da kekara yawan arzikin Nijeriya," in ji Tomori, amma bai bayyana yaushe wadannan ka'idoji za su fara aiki ba.
Sai dai kuma, a makon da ya gabata, ministan cigaban albarkatun kasa, Dele Alake ya ce a yanzu ya zama wata manufa ta gwamnati a saka sharadin amfanar da kasa sosai kafin a baiwa wani kamfanin hakar ma'adanai lasisi a Nijeriya.
Hakan na da manufar ganin an taimaka wa jama'ar yankunan da ake hakar ma'adanan.
Alake, wanda ke shugabantar kungiyar dabarun hakar ma'adanai ta Afirka da ta hada ministocin kasashen Uganda, Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Sierra Leone, Somalia, Afirka ta Kudu, Botswana, Zambia da Namibia, ya ce suna kokarin ganin albarkatun kasa a Afirka na amfanar jama'ar yankunansu.
Nijeriya, kasar da ta fi kowacce samar da makamashi a Afirka, na ta gwagwarmayar ganin ta amfana sosai da albarkatun kasar da take da shi wanda a baya rashin karfafa gwiwar masu zuba jari ke hana ta amfana da su.
Bangaren hakar ma'adanai da bai samu ci gaba ba a kasar nabayar da kasa da kaso daya na kudaden shigar da Nijeriya ke samu.
A shekarar da ta gabata Nijeriya ta fitar da sinadaran yin gwangwani mafi yawa zuwa China inda ta samu dala biliyan $108.34, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar ta sanar.
Gwamnatin Nijeriya na da manufar samun karin zuba jari a bangaren hakar ma'adanai ta hanyar bayar da lasisi ga kamfanonin da za su sarrafa su a cikin gida.
Gwamnatin ta samar da hukumar kula da ma'adanai tare da ba wa kamfanonin kaso 75 na ruwa da tsaki a harkar hakar ma'adanan, inda ta kuma samar da yanayin tsaro na musamman.
Gwamnatin na kuma kokarin kawo ka'idojin gudanarwa ga kananan masu hakar ma'adanai da suka yi wa a fannin, za a mayar da su kamar kungiyoyi.