Yawan harajin da Nijeriya ta karba ya kai naira tiriliyan 5.5 kwatankwacin dala biliyan bakwai kenan daga watan Janairu zuwa Yunin 2023, wanda shi ne mafi yawa da aka taba samu cikin wata shida, a cewar hukumar tattara haraji ta kasar.
Hukumar ta bayyana haka ne ranar Alhamis, a yayin da gwamnatin kasar ke daukar matakan karbar harajin a dukkan fannoni domin karfafa tattalin arzikinta.
Shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS Muhammad Nami, ya yi hasashen cewa harajin da za a karba a shekarar 2024 zai kai naira tiriliyan 25, wato dala biliyan 31.6 kenan, inda zai ninka yawan na 2022 sau biyu.
Nijeriya ta shirya yi wa tsarin karbar harajinta garanbawul, wanda mutane ba sa son bayarwa, sannan ta fadada dabarunta ta hanyar kawar da duk wasu abubuwa da ke jawo mata tarnaki wajen cimma a kalla kashi 18 cikin 100 na samun harajin da zai shiga ma'aunin tattalin arziki na GDP cikin shekara uku.
Nijeriya wacce ita ce mafi karfin tattalin arziki a Afirka na daga cikin kasashen da ba sa samun kudaden haraji sosai a duniya.
Gwamnatin kasar ta sha cewa tana son bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga don rage ciyo bashin kudi wajen aiwatar da ayyukan al'umma.
Aiki mai wahala
Samun kudade daga karbar haraji abu ne mai wahala a kasar da yawanci ba a yi wa kananan sana'o'i rajista ba.
"An samu wannan nasara a rabin shekara ne sakamakon hadin kan da aka samu daga masu biyan haraji a karan kansu... da kuma irin kokarinmu tare da masu ruwa da tsaki a dukkan fannoni masu rajista da marasa ita," in ji Nami.
Harajin da aka samu ba ta fannin fetur ba ya kai naira tiriliyan 3.76, yayin da fannin fetur ya samar da naira tiriliyan 2.03 na haraji a cikin wata shidan, kamar yadda Nami ya fada a cikin wata sanarwa.
Nami ya kuma kara da cewa samar da sabon tsarin karbar haraji a zamanance ya taimaka wajen tattara kudaden.
Ya kara da cewa hukumar FIRS na son samun naira tiriliyan 7.5 (dala biliyan 9.5) a cikin wata shidan da suka rage na 2023. Sannan yana hasashen samun harajin naira tiriliyan 25, (dala biliyan 31.6) a 2024.
Karuwar kudaden haraji
An samu karuwar kudaden harajin ne tun a shekarar 2020 a lokacin da kullen annobar korona da matsin tattalin arziki suka sa yawan kudaden haraji da ake karba suka ragu zuwa naira tiriliyan 4.95 (dala biliyan 6.3).
A shekarar 2022, yawan kudaden haraji da aka karba ya kai kashi 56 cikin 100 zuwa naira tiriliyan 10 (dala biliyan 12.6), wanda shi ne mafi yawa a tarihi, inda ya karu daga naira tiriliyan 6.4 (dala biliyan 8.1) na shekarar 2021.
A cikin gomman shekaru, Nijeriya ta mayar da hankali wajen daukar tsauraran matakan sauye-sauye da suka hada da cire tallafin man fetur da take kashewa makuda kudade, da kuma sanya dokoki na takaita kasuwancin kudaden kasashen waje, wani abu da Shugaba Bola Tinubu ke fatan a hankali za su bunkasa tattalin arziki.