Tuni dai aka fara jigilar danyen mai a matatar Dangote ta Nijeriya / Hoto: AFP

Asiya ce nahiyar da ke kan gaba wajen sayen fetur da ke da ƙarancin sinadarin sulphur (LSSR) na matatar Dangote a shekarar 2024, kamar yadda bayanai suka nuna, sai dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa adadin man da ake shigarwa zai ragu a watanni masu zuwa.

Fitar da mai na LSSR daga sabuwar matatar ta Dangote na iya taimakawa wajen rage matsalar ƙarancin mai a Asiya, nahiyar da ke da ƙarancin fetur mai sinadarin sulfur da ake buƙata yalwata Singapore, wato babbar cibiyar jiragen ruwa a duniya.

Kimanin metrik ton 500,000 na LSSR ne suka isa nahiyar Asiya daga Nijeriya a wannan shekarar zuwa yanzu, yayin da ake sa ran ƙarin tan 255,000 za su isa a watan Satumba, kamar yadda bayanan kamfanin bincike na Kpler suka nuna.

Amurka ita ce yanki na biyu mafi girma da ake shigar da man matatar Dangote, inda yawan adadin da aka shigar zuwa Arewacin Amurka da Tsibirin Caribbean ya kusan kai wa tan 700,000 a wannan shekara.

Sauƙin farashinsa ya taimaka wajen ƙara yawan jigilar man a 'yan watannin nan, inda Asiya ta ƙarbi kayanta na farko a cikin watan Yuni, ko da yake dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa matatar Dangote za ta samar tare da fitar da ƙarancin man LSSR a nan gaba, yayin da take shirin ƙara yawan kayayyakin da ake fitarwa daga sassan tace manta.

''Tun da muka soma aikin tace mai a yanzu, yawan sinadarin mai na LSSR zai ragu matuka," a cewar wanin babban jami'in kamfanin Dangote, yana mai kari da cewa babu wahala samun ɗanyen mai a yanzu.

Sarrafa ɗanyen fetur mai ƙarancin sinadarin sulphur irin na kamfanin West Texas Intermediate (WTI) yana samar da yawan LSSR, yayin da fitar da kayayyakin ya dogara ga buƙatun mai a cikin gida a Nijeriya, in ji Emril Jamil babban jami'in bincike kan mai a LSEG Oil Research.

"An sayi mai sosai daga WTI. Za mu samar da ƙarin man mai ƙarancin sinadarin sulphur LLSR yayin da ake ƙoƙarin haɓaka sassan tace mai," in ji Jamil.

''Da zarar an warware matsalar buƙatun cikin gida, akwai yiwuwar ba za riƙa samun yawan LSSR ba.''

Matatar man wadda ke samar da ganga 650,000 a kowace rana, kana mafi girma a Afirka, ta ƙara yawan ɗanyen man da ake shigo da shi Nijeriya a cikin yanayi na rashin wadatar man.

A yanzu haka dai ana kan gudanar da gwaje-gwaje a matatar don samar da albarkatun man fetur, a cewar kamfanin IIR Energy da ke nazari kan albarkatun ƙasa.

Reuters