Ma’aikatar Ci gaban Matasa ta Nijeriya ta bude damar ba da jari ga matasan kasar. / Hoto: AFP

Ma’aikatar Ci gaban Matasa ta Nijeriya ta bude damar ba da jari ga matasan kasar.

A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ma’aikatar ta ce wannan tsari ne da ke ƙarƙashin Asusun Ba da Jari ga Matasa wato Nigeria Youth Investment Fund, NYIF.

Ta ce an ware Naira biliyan 110 don ƙarfafa wa matasa a ɓangarori masu muhimmanci da za su kawo bunƙasar tattalin arziki.

Wannan tallafi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kai-komo tsakanin gwamnati da matasan ƙsar kan shirin zanga-zangar da matasan ke kira da a yi a watan Agusta mai zuwa.

Gwamnatin dai tana ta kiraye-kiraye ga matasan da su janye wannan aniya tasu, tana mai yi musu alkawarin ganin sauyi nan ba da daɗewa ba da kuma alkawarin cika musu muradunsu.

Sanarwar ta ce “KIRA GA MASU BUKATAR JARI: ASUSUN BA DA JARI NA MATASA YA DAWO”“Matasa ne ku masu sana’a da ke son bunƙasa sana’o’inku?

“Ma’aikatar Cigaban Matasa ta Gwamnatin Tarayya na farin cikin sanar da sake ƙaddamar da Asusun Jari ga Matasa na Nijeriya (NYIF).

"Ku nemi wannan tallafi yanzu don amfana da wannan babbar dama tare da haɓaka kasuwancinku.

”Ma’aikatar ta sanya adireshin intanet ɗin da za a shiga don neman tallafin a shafinta na X.

TRT Afrika