Kamfanin wanda mallakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya Elon Musk ne, yana samar da intanet hanyar amfani da tauraron dan'adam da ke karkashin kamfanin SpaceX. / Photo: Reuters

Hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa a kasar Ghana (NCA) ta ce kamfanin samar da intanet na Starlink yana aikace-aikace a cikin kasar ne ba bisa ka’idar doka ba.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ba ta bai wa kamfanin Starlink lasisi ba, sannan ba ta amince da duk wasu na’urori da kamfanin ke samarwa ba.

Kamfanin wanda mallakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya Elon Musk ne, yana samar da intanet hanyar amfani da tauraron dan'adam da ke karkashin kamfanin SpaceX.

Hakan yana nufin duk wani kamfani da ke sayar da kayayyakin kamfanin Starlink ko samar da intanet ta hanyar amfani da kamfanin Starlink yana sani cewa hakan ya taka dokar hukumar NCA, in ji sanarwar.

Kazalika hukumar ta gargadi al’ummar kasar da kamfanoni kan sayan duk wata na’ura ko yin hulda da kamfanin Starlink.

Sai dai a shafin intanet din Starlink, kamfanin ya bayyana cewa yana shirin samar da intanet a watanni na kusa da karshen 2024 a Ghana. Sai dai ya ce hakan ya dogara ne kan amincewar hukumomin kasar.

Akwai wasu ’yan kasuwa a kasar da ke sayar da kayayyakin kamfanin a Ghana, inda rahotanni ke cewa suna cajar GH¢1,100 zuwa GH¢18,000 daga masu amfani da intanet a kowane wata.

TRT Afrika