Kamfanin Ferrari na daga cikin kamfanonin sayar da motocin alfarma na duniya da suka shahara. Hoto/Reuters

Kamfanin sayar da motocin alfarma na Ferrari ya bayyana cewa zai soma karbar kudin kirifto domin sayar da motocinsa ga kwastamomi a Amurka.

Kamfanin ya ce yana sa ran nan gaba kadan zai kara fadada wannan shirin zuwa nahiyar Turai sakamakon karin bukatun yin hakan daga manyan kwastamomi, kamar yadda shugaban bangaren kasuwanci na kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kamfanin na Ferrari ya bayyana cewa ya yanke shawarar amfani da kirifto din ne sakamakon diloli da kwastamomin da ke sayen motocin na ta bukatar amfani da wannan tsarin saboda sun saka hannun jari a kirifton.

Manyan kamfanonin duniya da dama sun guji kirifto sakamakon yadda ake samun rashin tabbas na darajar kudin na intanet musamman bitcoin da sauran kudaden inda suke ganin kasuwanci da su ba lamari ne mai dorewa ba.

Haka kuma ka’idoji da ake yawan sakawa kan kirifto din na daga cikin abubuwan da suka hana bazuwarsa a matsayin hanyar biyan kudi.

Sai kuma fargabar da ake da ita kan na’urorin da ke hakar kirifto din na amfani da makamashi mai dumbin yawa wanda zai iya zama barazana ga muhalli shi ma wani dalili ne.

Misali kamfanonin motoci na Tesla a 2021 ya soma karbar bitcoin sai dai daga baya shugaban kamfanin ya dakatar da hakan saboda dalilai da suka shafi kiyaye muhalli.

Reuters