Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN) ta ƙulla yarjejeniya da matatar mai ta Dangote domin dakon mai kai-tsaye.
Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Alhaji Abubakar Garima ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja, bayan wani zaman kwamitin ayyuka na ƙungiyar ta ƙasa.
Shugaban ya bayyana cewa haɗin gwiwar za ta tabbatar da samun man fetur cikin sauƙi da rahusa a duk faɗin Nijeriya.
“Bayan ganawarmu da Aliko Dangote da tawagarsa a jihar Legas, muna farin cikin sanar da ɗaukacin al'umma cewa Matatar Dangote ta amince ta samar wa IPMAN man fetur na PMS, da man dizal da kuma kalanzir kai-tsaye domin rabawa a defo-defo da sauran gidajen mai.”
Garima ya buƙaci ‘yan ƙungiyar IPMAN da su mara wa Matatar Dangote baya, inda ya bayyana fa’idojin da ke tattare da hada-hadar da kuma tasiri mai kyau ga kasuwar canji a Nijeriya.
"Ya kamata 'yan kungiyar IPMAN su dogara da matatar Dangote da matatun man Nijeriya don samar da farar kaya, samar da ƙarin guraben ayyukan yi da kuma tallafawa sabon tsarin fatan Shugaba Bola Tinubu."
Wannan ci gaban na baya-bayan nan yana zuwa ne bayan shafe watanni ana shawarwari tsakanin bangarorin biyu, kuma ana sa ran hakan zai haɓaka inganci da araha, da haɓakar tattalin arziki.
Ana sa ran wannan yunƙuri zai kawar da shigar dillalai lamarin da kuma rage kuɗaɗen hada-hada tare da tabbatar da samun man fetur a-kai-a-kai ba tare da tsaiko ba.