Mataimakin shugaban kasar Nijeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin da zai fito da sabon albashi mafi karanci da za a biya ma'aikata a kasar.
An yi taron kaddamarwar ne a fadar gwamnatin kasar da ke Aso Rock, Abuja ranar Talata.
Kwamitin na da mambobi 37 kuma yana da bangarori uku, bangaren gwamnati da na masu zaman kansu, da kuma kungiyoyin kwadago na kasar, karkashin jagorancin Goni Bukar-Aji, tsohon Shugaban Ma'aikata na Kasa.
Mambobin kwamitin sun hada da ministan kudi, da na kasafin kudi, da kuma gwamnonin Bauchi da Neja da Anambra da Osun da Katsina, da Cross River. Sannan akwai shugabannin kungiyoyin kwadago guda biyu na kasar, NLC da TUC.
Da yake magana a madadin Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, Shettima ya ce, "Mun taru a nan don cika alkawarin inganta walwalar ma'aikata a Nijeriya, da ma kasa baki daya". Ya kuma bayyana cewa wannan kokari ne na samar da ma'aikata masu hazaka.
Shettima ya nemi 'yan kwamitin da su yi la'akari sosai kan karfin rukunan gwamnati wajen iya biyan albashin, yayin duba bukatun ma'aikata.
A tsarin mulkin Nijeriya, batun kayyade mafi karancin albashi, yana karkashin hurumin gwamnatin tarayya ne ita kadai, inda take da alhakin kayyade mafi kankantar albashi da za a biya a hukumance a fadin kasar.
A karshe, Kashim Shettima ya bukaci ministoci da shugaban ma'aikata na kasa da gwamnonin jihohi da su halarci tarukan kwamitin da kansu, sai dai idan hakan bai samu ba su tura wakilci.
A jawabinsa, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya nemi kwamitin su yi aiki bisa tsagwaron kishin kasa. Shi ma shugaban kwamitin, Goni Bukar-Aji ya sha alwashin amfani da kwarewarsu wajen aiwatar da aikin da aka dora musu nauyi.
Ana sa ran bayan fitar da rahoton kwamitin gwamnatin tarayya za ta mika wa majalisar dokokin kasar kudurin sabon albashi, wanda za a mayar doka a fadin kasar.