Ghana ta kaddamar da shirin noma na barbarar hannu don bunƙasa ayyukan noman koko a ƙasar /Hoto: AFP

Gwamnatin ƙasar Ghana ta bukaci manoma a yankunan da ke noman koko a fadin ƙasar da su ba da fifiko wajen amfani da tsarin noma na 'barbarar hannu' don bunƙasa amfanin koko.

Matakin hakan ya biyo bayan yunƙurin hukumar da ke kula da harkokin koko a Ghana 'COCOBOD' na karfafawa tare da tallafa wa ayyukan samar da waken koko masu inganci a ƙasar tare da tabbatar da cewa manoma da gwamnati sun samu riba mai tsoka daga amfanin gonakinsu.

''Amfani da tsarin noma na barbarar hannu da kuma tsaftace ayyukan noma kamar sare itace da ciyayi da kuma takin zamani za su taimaka wajen inganta yawan amfanin gona,'' in ji shugaban hukumar COCOBOD Mista Joseph Boahan Aidoo.

"Yanzu da farashin koko ke daɗa samun karbuwa da kyau a kasuwannin duniya, abin da ake bukata shi ne haɓaka amfanin gona don samun ribar manoma'' kamar yadda kamfanin dillacin labarai Ghana GNA ta ruwaito Mista Boahan na fadi a yayin kaddamar da shirin ''barbarar hannu'' noma na 2024 wanda aka yi a Nzema Ayinyinasi da ke yankin yammacin kasar a karshen mako.

Kazalika yunkurin ya biyo bayan ziyarar da hukumar ta kai gonaki da dama da kuma masarautu da suka ƙunshi manoma sama da 3,000 cikin kwanaki hudu, inda ya ce yanzu da kuma kaddamar da shirin noman ''akwai bukatar manoman koko su rungume shi,'' in ji shugaban.

Shirin tsarin noma na 'barbarar hannu' zai taimaka wajen ilimantar da kuma karfafa wa manoma wajen canza kwayar waken furen namijin koko zuwa macen daga wata bishiya zuwa wata ta hanyar amfani da hannu maimaikon barin kwari su yi aikin.

Hukumar COCOBOD ta bayyana cewa yawan amfanin noman koko da ake samu a yana tsakanin buhu biyar zuwa takwas kan kowace kadada, idan aka kwatanta da buhu 20 zuwa 30 a kowace kadada da ake samu a wasu gonaki a yankin yammacin Kudancin ƙasar ta hanyar amfani da tsarin noma na barbarar hannu.

Kazalika hukumar ta buƙaci manoma da su dauƙi noman koko ba kawai a matsayin hanyar rayuwa ba amma a matsayin sana’a, tare da kara himma da kuma zuba jari don samun riba mai tsoka

Haka kuma shugaban hukumar ta COCOBOD ya shawarci manoma da su riƙa rage bishiyar kokon su akai-akai don samar da yanayi mai kyau da kuma hana cututtuka da ɓarnar ƙwari.

TRT Afrika