Shugabar Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), Olubunmi Kuku, ta bayyana cewa filayen jiragen sama uku ne kaɗai daga cikin 22 waɗanda ake zirga-zirgar cikin gida da ƙasashen waje suke cikin yanayin da za a iya hada-hadar kasuwanci tare da samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar.
Yawancin filayen jiragen sama 22 da ke ƙarƙashin kulawar hukumar FAAN na buƙatar gyare-gyare sosai tare da muhimman ababen more rayuwa kamar samar da harabar zaman fasinjoji da hanyoyin jiragen sama masu inganci, a cewar shugabar hukumar.
Hukumar FAAN tana ba da tallafi ga filayen jiragen saman Nijeriya guda 19 saboda ba sa samun zirga-zirgar fasinjoji daidai da kuɗin da ake kashewa wajen gudanar da ayyukansu, kamar yadda Olubunmi Kuku ta bayyana a wani shirin gidan talbijin na Channels a Nijeriya a ranar Talata.
“Muna da filayen tashi da saukar jiragen sama guda 22 waɗanda suke karkashin kulawarmu, sannan akwai wasu kusan shida ko bakwai da suke mallakin gwamnatocin jihohi ne ko na 'yan kasuwa masu zaman kansu, waɗanda suma muke tallafa musu ko dai ta hanyar tsaron jiragen saman ko na kashe gobara da ceto,” in ji Kuku.
Ta kara da cewa, ''Muna da jihohi da dama a arewa da kuma kudu maso yamma da ke gina sabbin filayen jiragen sama. Zan iya cewa bisa ga ƙididdigar da muke da shi yanzu, a zahiri uku ne kawai daga cikin filayen jiragen sama 22 suke samar da riba da gudummawa sosai ga a ayyukan tashoshin filayen jirage da muke gudanarwa.''
Shugabar ta bayyana cewa hanyoyin sauka da tashin jaragen saman sun tashi daga aiki sakamakon wuce tsawon lokacin 20 kana akwai buƙatar a sabbunta tare da inganta su.
Kazalika Kuku, ta ba da shawara kan cewa ayyukan bunƙasa tattalin arziki a jihohin da ke da filayen jiragen sama suna samuwa ne tare da zirga-zirgar fasinjoji yadda ya kamata maimakon gina sabbin filayen jiragen sama.
Ta ce, ya kamata gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen inganta masana'antu da kasuwanci da kuma fannin yawon buɗe ido a yankunansu don bunƙasa zirga-zirgar fasinjoji da kuɗaɗen shiga.
Hukumar FAAN na ware kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen shigar da take samu ga gwamnatin tarayya, wanda hakan ke haifar da babban ƙalubale, in ji shugabar, tana mai ƙari da cewa hukumar tana kan tattaunawa da ɓangarori daban-daban na gwamnati domin lalubo hanyoyin da za a ɗauka na samun sauƙi.