Jirgin Habasha wato Ethiopian Airlines./ Hoto: AFP

An dakatar da duka zirga-zirgar jiragen saman Habasha zuwa Eritiriya, daga ranar 30 ga watan Satumban 2024, in ji sanarwar da kamfanin jiragen saman Habasha wato 'Ethiopia Airlines'.

A cewar sanarwa wadda kamfanin da ke yankin gabashin Afirka ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, ya ce ya samu wasika daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Eritiriya kan wannan mataki.

Kamfanin ya ƙara da cewa, ''ba a bayyana masa taƙamaiaman dalilan da suka sa aka dakatar da ayyukan jiragen saman ba.''

"A halin yanzu kamfanin jirgin na Habasha dai yana neman ƙarin haske daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Eritriya, kana ya ƙuduri aniyar warware duk wata matsala cikin lumana da gaggawa," in ji sanarwar.

Ko da yake dai kamfanin bai raba kwafin wasikar da ya samu daga Hukumar Kula da Sufurin jiragen Sama ta Eritiriya ba.

Amma kamfanin jiragen Habasha ya yi alkawarin samar wa abokan cinikinsa ƙarin bayani game da duk wani ci gaba da aka samu game da lamarin.

TRT Afrika