An sayar da Bitcoin a kan $40,700 da misalin karfe hudu na safe a agogon GMT ranar Litinin. / Hoto: AA

Farashin kowanne kudin kirifto na Bitcoin ya kai $40,000 ranar Litinin din nan a karon farko tun watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan da masu mu'amala da shi suka samu kwarin gwiwa cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta bari a rika amfani da shi wajen harkokin kasuwanci.

Darajar kudin na kirifto ta tashi sosai a wannan shekarar, inda ta ninka da kusan kashi 150, bayan da mutane suka samun kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan hukumomin da ke sanya ido kan hada-hadar kudi za su bari a soma amfani da shi.

Hakan zai sa a rika bibiyar farashin kudin na bitcoin da kuma barin jama'a su sanya hannun-jari a cikinsa kai-tsaye.

"Wannan manufa ta amfani da wannan kudi a kasuwanni hannun-jari... ana sa rai sosai kuma hakan zai daukaka darajar bitcoin," in ji Lucy Guzmararian, mai kamfanin Token Bay Capital, a hirarta da Bloomberg.

An sayar da Bitcoin a kan $40,700 da misalin karfe hudu na safe a agogon GMT ranar Litinin.

AFP