Hakan na faruwa ne a yayin da aka samu labari cewa Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin kuɗi ta Birtaiya ta ce za ta bari a ƙirƙiro takardun lamuni da ke da alaƙa da kuɗaden kirifto. / Hoto: AA

Darajar kuɗin kirifto na Bitcoin ta yi ƙaruwar da ba ta taɓa yi ba inda a ranar Litinin kowanne ɗaya ya kai $71,000 sakamakon ƙarin masu buƙatar kuɗin a daidai lokacin da Baitulmalin Amurka yake shirin rage kuɗin-ruwa na wannan shekarar.

An riƙa sayar da kowanne Bitcoin a kan $71,432 a kasuwar hada-hadar kuɗi ta yankin Asiya, a cewar alƙaluman da Bloomberg ta fitar, abin da ke nufin ya tashi da fiye da kashi 70 cikin ɗari a wannan shekarar.

Hakan na faruwa ne a yayin da aka samu labari cewa Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin kuɗi ta Birtaiya ta ce za ta bari a ƙirƙiro takardun lamuni da ke da alaƙa da kuɗaden kirifto.

Ta ɗauki matakin ne bayan a wannan shekarar hukumomi a Amurka sun nuna amincewarsu kan amfani da hannayen-jari da ke da alaƙa da kuɗaɗen kirifto na Bitcoin, abin da ya sa manyan masu zuba hannun-jari suka rungume shi.

AFP
Reuters