Kazalika farashin dalar a babban shafin kasuwar musayar kudade ta bayan fage AbokiFX a ranar Laraba ya kai 1,515. 

Darajar kudin Nijeriya naira ta sake faɗuwa warwas a kan dala a hukumance, kamar yadda bayanan cibiyar bin diddigin musayar kuɗaɗe ta FMDQ da ke Legas suka nuna a ranar Laraba.

Bayanan FMDQ sun nuna cewa farashin dalar ya kai 1,531, kuma yana sassauyawa ta hanyar ƙaruwa da gaggawa.

Kazalika farashin dalar a babban shafin kasuwar musayar kudade ta bayan fage AbokiFX a ranar Laraba ya kai 1,515.

Tun da aka shiga sabuwar shekarar nan ta 2024 naira ta rasa kashi 40 cikin 100 na darajarta. Farashinta a hukumance ma yana ta sauka yana kusa kamo farashinta a kasuwar bayan fage saboda ƙarancinta da ake yi a ƙasar.

Reuters