Nijeriya na neman cimma burin samar da fetur mai yawa a 2024. Hoto: Reuters

Da wuya Nijeriya, wadda mamba ce a ƙungiyar ƙasashe masu samar da man fetur OPEC, ta iya cimma ƙudurinta na samar da yawan fetur ɗin da ake so a shekarar 2024, bayan tsawon shekaru na raguwar abin da take samarwa, a cewar alkaluman biyu daga cikin kamfanoni uku da ƙungiyar ta ɗorawa alhakin tantance abubuwan da ƙasar ke fitarwa gabanin yanke shawara kan manufofi.

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da ƙawayenta irinsu Rasha da ake kira OPEC+ ta jinkirta taronta na baya-bayan nan sakamakon rashin jituwar da aka samu kan rabon yawan man fetur da ƙasashen Afirka da suka hada da Nijeriya da Angola za su samar, in ji majiyoyi.

Nijeriya na neman cimma burin samar da fetur mai yawa a 2024, wanda OPEC+ ta tabbatar a daidai lokacin da ƙungiyar ke tunanin rage yawan albarkatun da ake fitarwa maimakon ƙarawa.

A watan Yuni, OPEC+ ta rage yawan man da Nijeriya za ta haƙo na shekarar 2024 zuwa ganga miliyan 1.38 a kowace rana daga miliyan 1.74 na shekarar 2023, lamarin da ke nuna cewa tsawon shekaru Nijeriya ta kasa cimma burinta.

Sai dai kungiyar, ta amince ta bai wa Najeriya kason fitar da gangar mai da ya kai miliyan 1.58 a shekarar 2024, idan har an tabbatar da cewa za ta iya fitar da yawan da ya kai hakan.

Nijeriya na neman haɓaka albarkatun man fetur ta hanyar farfaɗo da rijiyoyin man da suka zam kamar kufai da kuma ƙara yawan haƙo shi, kuma tana ɓullo da sabbin matakai don magance barazanar tsaro.

OPEC+ ta bai wa wasu kamfanoni masu ba da shawara guda uku masu zaman kansu - IHS da Rystad Energy da Wood Mackenzie aiki - don tabbatar da ko Nijeriya, da Angola da Kongo, za su iya kaiwa matakin fitar da yawan man aka yi niyya a shekarar 2024. Za su bayar da rahoton sakamakonsu a taron OPEC+ na ranar Alhamis.

Reuters