A ranar 1 ga watan Mayu ne Bitcoin ɗin ya yi warwas inda ya dawo ƙasa da $57,000 a karon farko cikin sama da watanni biyu. / Hoto: Reuters

Bitcoin a ranar Juma’a ya ƙara daraja inda kowane guda ɗaya ya wuce $67,000 a karon farko cikin sama da mako uku.

Lokaci na ƙarshe da nau’in kuɗin na kirifto ya kai haka tun 24 ga watan Afrilu.

An rinƙa sayar da Bitcoin ɗin a wannan farashin har zuwa misalin ƙarfe takwas na dare agogon GMT, kamar yadda bayanai daga CoinMarketCap suka tabbatar.

Sannan sai Ethereum, wanda shi ne altcoin mafi girma a duniya ya ƙaru da kusan kaso 5.2 cikin 100 inda kowane ɗaya ya kai har $3,090 da misalin 8:37 na dare agogon GMT, inda wasu daga cikin nau’in na altcoins suka samu tagomashi da har zuwa kaso 10 cikin 100.

A halin yanzu darajar kuɗin kirifto a duniya baki ɗaya ta kai tiriliyan $2.42 inda take samun ƙaruwa da aƙalla kaso 3.12 cikin 100 a kullum.

A ranar 1 ga watan Mayu ne Bitcoin ɗin ya yi warwas inda ya dawo ƙasa da $57,000 a karon farko cikin sama da watanni biyu, wanda hakan shi ne mataki mafi ƙasa da ya taɓa samun kansa tun daga 27 ga watan Fabrairu.

Kasuwar kirifto ta shiga wani yanayi a lokacin bayan masu zuba jari sun yi matuƙar raguwa a watan da ya gabata, inda aka yanke wa tsohon shugaban Binance ɗaurin wata huɗu a gidan yari.

Tagomashin da kirifto ɗin ya samu na zuwa ne bayan hauhawar farashi a Amurka a watan Afrilu ya ragu idan aka kwatanta da watan da ya gabata, wanda hakan ya sa masu zuba jari suka sa rai kan gwamnati za ta rage kuɗin ruwa a watan Satumbar nan.

AA