Manyan kamfanin da matakin ya shafa a cewar bayanan sun hada da Binance, da Forextime, da OctaFX, da Crypto, da FXTM, da Coinbase, da kuma Kraken / Hoto: AA

Rahotanni a Nijeriya sun ce tuni aka fara rufe manhajojin hada-hadar kudade na intanet, ko kuma cryptocurrency a Turance, bisa umarnin hukumomin ƙasar, a wani mataki na daƙile hauwhawar farashin dala da faduwar darajar naira.

A jiya Laraba ne hukumomi suka bai wa kamfanonin waya na kasar umarnin toshe damar shiga manhajojin, domin hana masu hada-hadar kudade ta intanet damar shiga su yi cinikayya.

Masu musayar kudade a kasar da kuma hukumomi na zargin masu hada-hadar kudi ta intanet da ba da gagarumar gudunmuwa wajen tashin farashin dala a kasar, abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani mawuyacin hali.

Wata majiya daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Nigeria NCC ta tabbatarwa TRT Hausa cewa an bai wa kamfanoni na waya umarnin daukar matakin, kuma har ma an fara aiki da shi, musamman ga masu amfani da waya.

Wasu jaridun Nijeriya sun rawaito cewa kamfanonin sadarwa na kasar sun tabbatar da samun umarnin daga NCC don su dauki matakin.

Manyan kamfanin da matakin ya shafa a cewar bayanan sun hada da Binance, da Forextime, da OctaFX, da Crypto, da FXTM, da Coinbase, da kuma Kraken.

To sai dai su ma a na su bangaren, tuni kamfanoni na hada-hadar kudaden ta intanet suka fara daukar matakan daƙile cinikayya tsakanin dala da naira barkatai.

Wannan matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin matakan da take dauka don magance tashin farashin dala, abin da yake haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a kasar.

Batun dai na ci gaba da janyo damuwa a tsakanin yan kasar baki daya, musamman masu ƙaramin ƙarfi, wadanda a mafi yawan lokuta abincin da za su ci a cikinsu ke gagararsu.

TRT Afrika da abokan hulda