Ofishin da ke Kula da Basussukan Nijeriya DMO ya ce jumullar bashin da ake bin ta ya zuwa ranar 30 ga watan Satumban 2023 ya kai naira tiriliyan 87.91, kwatankwacin dala biliyan 114.35.
A wata sanarwa da DMO ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa kudaden na wakiltar basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja ne na cikin gida da na waje.
Ofishin Kula da Basussukan ya ce bashin ya nuna ɗan ƙarin da aka samu na kashi 0.61% idan aka kwatanta da naira tiriliyan 87.38 na ranar 30 ga watan Yunin 2023.
"An bayyana wannan yanayin ne ta hanyar raguwar Bashin Kasashen Waje daga dala biliyan 43.16 daga ranar 30 ga Yunin 2023 zuwa dala biliyan 41.59 na ranar 30 ga Satumban 2023, da kuma wani matsakaicin karuwar naira tiriliyan 1.80 a cikin Bashin Cikin Gida," kamar yadda sanarwar ta sanar.
“Bashin na waje ya ragu ne saboda ƙasar ta biya takardun lamuni na dalar Amurka miliyan 500 da kuma biyan dala miliyan 413.859 a matsayin babban biya na farko na lamunin dala biliyan 3.4 da aka samu daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF a shekarar 2020 yayin annobar Covid-19.
“Kudin ruwan da ake biya a kan waɗannan basussuka da na sauran basussuka, nuni ne ƙarara na jajircewar Gwamnatin Tarayya na mutunta bashin da ake bin ta.
"Duk da haka, shirye-shiryen da Shugaban Kasa ya yi don samar da kudaden shiga suna da muhimmanci ga daidaiton kasafin kudin Nijeriya baki daya," a cewar DMO.