Bankin raya ƙasar China (CDB) ya amince da ba da rancen lamuni na Euro miliyan 245, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 254.76, don tallafa wa aikin gina layin dogo da zai hada jihar Kano zuwa Kaduna a Nijeriya.
A wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Talata, ya ce rance zai taimaka wajen ba da tallafin kudin da ake bukata don kammala aikin layin dogon a kan lokaci.
Kamfanin gine-gine na China (CCECC) ne zai gudanar da aikin tare da tallafin kudin da bankin CDB zai bayar.
Kazalika ana sa ran kuɗaɗen za su taimaka wajen sauƙaƙa hanyoyin bunƙasa sufurin jiragen ƙasa na Nijeriya, tare da inganta ci gaban tattalin arziki da cudanya tsakanin jihohin biyu a kasar.
Tsawon aikin hanyar layin dogon da zai hada Kano zuwa Kaduna ya kai kilomita 203, kuma da zarar an kammala shi, zai samar da hanya kai tsaye wadda zata hada Kano zuwa babban birnin ƙasar Abuja.
“Haka kuma aikin zai inganta ci gaban masana’antu masu bukatar hada-hadar ta hanyar, tare da samar da guraben ayyukan yi da dama ga al'ummar Nijeriya,'' in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa “an sanya aikin a cikin jerin ayyukan da za a mayar da hankali akan su a taron ƙasa da ƙasa na haɗin gwiwa tattalin arziki karo na uku na Belt and Road Forum.”
Mataki na gaba da aka sa a gaba a cewar Bankin CDB, shi ne haɗa kai da Nijeriya domin tabbatar da an ci gaba da samun lamunin da za a gudanar da aikin yadda ya kamata ba tare da wani tsaiko ba.
Da zarar an kammala aikin, layin dogo zai bai wa mazauna wuraren aminci da kuma hanyar sufuri mai sauki, yanayin da ake fatan zai inganta haɗin gwiwar yanki sosai.