Kamfanin Apple ya sanar da cewa ya gano wasu dalilai kadan da suka sa sabbin wayoyin IPhone ke daukar zafi fiye da yadda aka yi zato.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kamfanin na cewa daga cikin dalilan har da wata matsala da ke tattare da manhajar iOS 17 wadda ake sa ran gyarawa idan za a sabunta manhajar a nan gaba.
Bayan korafin da aka rinka yi kan cewa sabbin Iphone din na daukar zafi, Apple ya bayyana cewa wayoyin na daukar zafi a kwanakin faro bayan kammala daidaita wayar da kokarin dawo da abubuwan da ke cikin tsohuwar wayar mutum wanda hakan zai kara ayyukan da wayar ke yi.
Kamfanin na Apple ya bayyana cewa wata matsala da ke sa wayoyin na daukar zafi ita ce wasu manhajoji da aka sabunta na wasu kamfanoni wadanda ke neman cika wayar.
Apple ya ce yana tattaunawa da masu manhajojin domin ganin yadda za a yi domin gyara matsalolin. Wasu daga cikin manhajojin da ke jawo matsalar sun hada da Asphalt 9 da manhajar Instagram da Uber, kamar yadda kamfanin ya bayyana.
Instagram ya gyara matsalar da ke tattare da manhajarsa tun a ranar 27 ga watan Satumba.
Gyaran da za a yi wa iOS 17 ba zai rage kuzari da aikin wayar ba sai dai gyara matsalar daukar zafi da take yi, in ji kamfanin.