Wasu bankunan sun kayyade ko takaita adadin kudaden da za su iya bayarwa / Hoto: Reuters

Bayanai daga Jamhuriyar Nijar na cewa ana fuskantar matsalar karancin kudi a bankunan kasar sakamakon matakin da Babban Banki na BCAO ya dauka na hana bankunan samun wadatattun kudade.

Hakan ya biyo bayan jerin takukuman da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS da UEMOA suka kakaba wa kasar.

Hukumomin biyu sun sanya takukuman ne sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.

Wasu bankunan sun takaita adadin kudaden da za su iya bayarwa, yayin da wasu suka ce za su ba da kudi ne bayan sun yi nazari kan abin da mutum yake bukata.

Rashin samun isassun kudaden a bankuna ya haddasa koma-baya a harkokin kasuwanci da kuma matsi ga rayuwar jama'a, a cewar Elhaji Sani Shekarau, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Nijar.

Ya shaida wa TRT Afrika cewa “Kanana da manyan 'yan kasuwa sun shiga cikin mawuyacin yanayi saboda yanzu dan kasuwa ba zai iya aika kudi ba kuma ba a iya aiko masa sakamakon wannan matakin da bankunan suka dauka.”

Sai dai da yake zantawa da TRT Afrika, shugaban kungiyar ma'aikatan bankuna kasar wato SYNBANK, Malam Abdoul'aziz Mahamadou ya ce ba wai babu kudin a bankuna ba ne, kawai sun dauki wannan matakin ne a bisa umurni kungiyoyin ECOWAS da UEMOA.

“An yi hakan ne domin takaita adadin kudin da mutum zai iya dauka don a hanawa masu zuwa bankunan da niyyar su dauki kadade masu yawa su kai gida su boye.

“Kuma wannan matakin da bankunan suka dauka zai sa duk wanda ya je bankin zai samu kudin daidai gwargwado,” in ji Malam Abdoul'aziz.

Kawo yanzu sojojin Jamhuriyar Nijar na fuskatar matsin lamba a kan su mayar da kasar kan tafarkin dimokuradiyya, kuma su gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa.

Ko a taronta na baya-bayan nan, ECOWAS ta sake jaddada matakan takunkuman da ta kakaba wa Nijar tare da saka sojojin kungiyar cikin shirin ko ta kwana idan ta kama ayi amfani da karfin soja a kan sojojin da suka yi juyin mulkin.

TRT Afrika