Ministan Harkokin Ma'adinai na Nijeriya Dele Alake

Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai game da ma'adinai da sauran albarkatun ƙasa da Allah ya huwacewa ƙasar.

Da yake ƙaddamar da shafin na intanet, Ministan Harkokin Ma'adinai na Nijeriya Dele Alake ya ce sun ɗauki matakin ne domin rage wahalhalun da masu zuba jari daga ƙasashen waje suke sha wurin samun bayanai game da ma'adinan da ƙasar take da su.

"A baya mutumin da ke son zuba jari sai ya zo Nijeriya da kansa kafin ya samu bayanan da yake buƙata, amma yanzu yana iya samun waɗannan bayanai a shafin intanet sannan ya yanke hukunci kan ko zai zuba jari," a cewar Ministan.

Nijeriya ce kan gaba a albarkatun man fetur a Afirka, kuma tana da tarin arzikin sauran albarkatun ƙasa irin su zinare, kuza, tama da ƙarafa, kwal, farar ƙasa, da sauransu.

Ana iya samun shafin na intanet, mai suna Nigeria Mineral Resources Decision Support System (NMDSS), a https:/miningdecision.minesandsteel.gov.ng/nmrdss/. kuma yana ɗauke da bayanai kan dukkan ma'adinan da Nijeriya take da su da jihohin da ake samunsu da ma duk wasu bayanai kan yadda za a zuba jari a kan su.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sha alwashin bunƙasa fannin ma'adinan Nijeriya domin samun kuɗaɗen-shiga da rage dogaro da man fetur, tana mai cewa a halin da ake ciki wannan fanni ba ya samar da sama da kashi ɗaya na kuɗin-shigar ta.

A kwanakin baya ne Ma'aikatar Harkokin Ma'adinai ta Nijeriya ta gudanar da garambawul inda ta amince ta bai wa masu zuba jari kashi 75 na hannun-jarin kamfanin haƙar ma'adinai na ƙasar, tare da hana fitar da ma'adinan da ba a sarrafa ba, da haramta kamfanonin da ke haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

TRT Afrika