Shugaban Kasar Amurka Joe Biden a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa yana da niyyar kawo karshen shigar kasashen Gabon da Nijar da Uganda da Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin Shirin Dokar Cigaban Afirka da Damarmaki (AGOA).
Biden ya ce zai dauki wannan mataki ne saboda 'keta dokoki' da take hakkokin dan'adam da gangan da Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya da Uganda ke yi.
Ya kuma bayyana gazawar Nijar da Gabon wajen kare walwalar siyasa da dokokin kasa.
Biden ya bayyana cewa zai ci gaba da duba yiwuwar ko kasashen sun cika ƙa'idojin kasancewa a cikin shirin.
AGOA da aka kaddamar a 2000, na bayar da dama ga kamfannin Amurka su shigar da kayayyaki daga wasu kasashen waje ba tare da biyan haraji ba.
A watan Satumban 2025 ne wannan doka za ta zo karshe, amma ana ci gaba da tattaunawa kan ko za a kara wa'adinta, kuma zuwa yaushe ne za a kara.
Gwamnatoci da masana'antun Afirka na rajin a kara wa'adin na tsawon shekaru goma, don sake tabbatuwar kasuwanci da masu zuba jari da suke da damuwa game da makomar AGOA.