Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa, an cimma matsaya a yarjejeniyar matakin ma'aikatansa da Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo a nazarin karshe da aka yi kan shirin ba da lamunin dalar Amurka biliyan 1.5 a ranar Laraba.
IMF dai ya bukaci kasar Kongo da ta yi amfani da kudaden yadda suka kamata a yarjejeniyar hakar ma'adinai da aka yi wa kwaskwarima.
A karon farko wannan yunƙuri ya kai Congo kusa da matakin karshe na kammala shirin IMF, ko da yake yarjeniyoyin baya sun gamu da kalubale musamman nuna rashin gaskiya a fannin hakar ma'adinan da aka yi.
"Baki ɗaya an yi nasara a ayyukan shekaru uku da aka ware karkashin shirin, tare da cimma mafi yawan manufofin da aka saka a gaba da kuma aiwatar da muhimman gyare-gyare, duk da cewa aikin ya dauƙi tsawon lokaci," a cewar IMF cikin wata sanarwa da aka fitar.
Da zarar hukumar IMF ta amince da hakan, yarjejeniyar za ta ba da damar fitar da kason karshe na kusan dala miliyan 200.
Kamfanonin China
IMF ya bayyana cewa- babbar kasar da ke samar da dutsen cobait a duniya- ma'adanin da ake amfani da shi wajen haɗa wayoyin zamani - kana kasa ta uku mafi girma wajen samar da azurfa, dole ta sa ido kan tasirin haɗin gwiwar kamfanin Sicomines da kamfanonin kasar China na kwanan nan a dokar kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi wa kwaskwarima.
''Kazalika, ana buƙatar a samar da wasu hanyoyi don tabbatar da an yi amfani da wadannan kudade yadda suka kamata,'' in ji IMF.
Shugaban kasar jamhuriyar Demokradiyar Kongo Felix Tshisekdi ya buƙaci a sake fasalin yarjejeniyar samar da ma'adinai ta 2008 na kamfanin Sinohydro Corp da kuma China Tailway Group don samar da karin fa'idoji ga kasar.
A watan Maris ne aka sanya a hannu kan yarjejeniyar.
''Hukumar IMF tana nuna damuwarta ne bisa ga hanyoyin da za a bi wajen amfani da wadannan kudade kuma ta bukaci a biya cikin asusun baitul malin kasar maimakon wata hukuma ta daban ta sarrafa su kamar yadda ake yi a baya,” kamar yadda wani jami’in ma’aikatar kudi a kasar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Sanarwar Kwangiloli
Sanarwar kwangiloli kan ma'adinai na ɗaya daga cikin sharuddan shirin IMF, a makon da ya gabata ne Kongo ta fitar da cikakkun bayanai da aka daɗe ana jira game da sharuddan yarjejeniyar Sicomines da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya haɗa kusan dala biliyan bakwai na zuba jarin kayayyakin more rayuwa daga ɓangaren China idan har farashin azurfa ya ci gaba da hauhawa.
A yarjejeniyar baya da aka yi, an yi alkawarin zuba jarin kayyayakin more rayuwa na dala miliyan 822 kadai daga cikin dala biliyan 3, a cewar wani rahoto na shekarar 2023 da sashin binciken kudi na kasar Congo ya fitar.
Har ilau yarjejeniyar da aka yi wa kwaskwarima ta ƙunshi wasu sharudda da 'yan Kwango da kuma ƙungiyoyin fararen hula na duniya ke ganin ba su da wani amfani ga kasar.
Daga cikin kuwa har da hana kamfanin Sicomines daga biyan haraji har zuwa 2040.