A shekarar 2009 zuwa 2018 ne Jacob Zuma ya rike mukamin shugaban ƙasar Afirka ta Kudu na hudu . / Hoto: AP       / Photo: AFP

Ƙotun Tsarin Mulkin Afrika ta Kudu ta yi watsi da buƙatar ''gaggawa'' ta tsohon shugaban ƙasarJacob Zuma wanda ya nemi a ɗakatar da zaɓen shugaɓan ƙasar da aka shirya gudanarwa a ranar Juma'a.

Zuma, wanda shi ne shugaban jam'iyyar uMkhonto weSizwe (MK), ya yi zargin an tafka kura-kurai a zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Jam'iyyar MK, wadda ta samu kujeru 58 na 'yan majalisar dokoki, ta zo ta uku a zaɓen, bayan jam'iyyar ANC mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA).

A yammacin ranar Laraba ne dai, Kotun Ƙolin Afirka ta Kudu ta yi fatali da buƙatar ''gaggawa'' ta jam'iyyar MK tana mai cewa ''ƙirƙirarriyar buƙata ce'' kana ba ta cancanta ba.

'Gaza gabatar da shaida'

A cewar Kotun Ƙolin, jam'iyyar MK ta gaza gabatar da shaidar cewa ''za ta fuskanci lahani mara misaltuwa idan har ba a dakatar da zaɓen ba."

Kazalika Kotun ta ce jam'iyyar MK ta gaza gabatar da shaidun da za su tabbatar da zargin da ta yi cewa an yi maguɗi a zaɓen ranar 29 ga watan Mayu.

'Yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu 400 ne za su kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasa ranar Juma'a, inda ɗan takara ke buƙatar ƙuri'u aƙalla 201 don yin nasara.

Jam'iyyar ANC ta samu kashi 40 cikin ɗari a zaɓen da aka gudanar a baya, lamarin da ya tilasta mata neman abokan ƙawance don kafa gwamnati.

TRT Afrika