Zimbabwe ta ayyana dokar ta-baci kan tsaftace muhallaci bayan an kwashe wata da watanni ba tare da kwashe tarkacen shara da ya mamaye ko'ina a fadin babban birnin kasar Harare ba.
Sanarwar wannan matakin da shugaba Emmerson Mnangagwa ya yi a ranar Litinin ta bai wa gwamnati damar karbar ragamar aikin kula da shara a birnin - aikin da majalisar karamar hukuma ta saba gudanarwa.
Gwamnati ta dora alhakin durkushewar aikin kula da sharar birnin kan gazawar majalisar karamar hukumar karkashin jagorancin ‘yan adawa wajen saka hannun jari a ayyukan kwashe shara da kayan aiki da kuma ma’aikata.
Ofishin lardin birnin Harare bai mayar da wani martani ga sanarwar ba.
Karbe iko
Hukumar kula da muhalli ta kasar za ta dauki nauyin tattara sharar da ta taru a manyan kantuna da unguwanni, a cewar sanarwar.
Kazalika za a girke rumbunan zuba shara a kan tituna da wuraren taruwar jama’a sannan hukumar kula da muhalli za ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a game da zubar da shara.
"Gwamnati ta lura tare da matukar damuwa game da mummunan yanayin rashin tsaftar da yankin ke ciki Harare," cewar sanarwar.
A farkon shekarar 2023 ne aka samu bullar cutar kwalara a Harare inda mutane da dama suka kamu da ita.
Yankin Lardin Harare ya hada birnin Harare da Chutungwiza da Epworth da kuma Ruwa – wadanda duk ke cikin manyan biranen da Zimbabwe ke takama da su.