'Yan sandan Nijeriya

'Yan sanda sun riƙa harba tiyagas kan ɗaruruwan masu zanga-zanga a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya da Abuja babban birnin ƙasar, sakamakon yadda ta rikiɗe zuwa fashe-fashe da satar kayayyaki.

Dubban mutane a birane daban-daban na Nijeriya suka hau kan tituna domin bayyana ɓacin ransu kan matsin rayuwar da suke ciki wanda ya yi ƙamari tun hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki a shekarar 2023.

Masu zanga-zangar, wadda ta ja hankalin 'yan ƙasar tun da aka sanar da ranar gudanar da ita, sun fantsama kan tituna a manyan birane irin su Lagos da Kano da Abuja.

Suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu kamar "A kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya", "A dawo da tallafin man fetur" da sauransu.

Sai dai bayanai daga sassa da dama sun nuna cewa mutane suna fuskantar katsewar intanet da kira a wayoyinsu.

A Abuja, babban birnin Nijeriya, masu zanga-zangar sun hau manyan tituna duk da umarnin da wata kotu ta bayar na taƙaita zanga-zangar a Babban Filin Wasa na Ƙasa.

Lauyan masu zanga-zangar, Barista Deji Adeyanju, ya shaida wa manema labarai cewa bai ga umarnin da kotun ta bayar ba, amma duk da haka yana rarrashin masu zanga-zangar su gudanar da ita a wurin da kotun ta iyakance musu.

Kwamishinan 'yansandan Abuja, Benneth Igweh, ya gargaɗi masu zanga-zangar kan rashin bin umarnin kotun, yana mai cewa sun ɗauki dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Daga bisani 'yan sanda sun harba tiyagas kan masu zanga-zanga bayan da suka nufi tsakiyar birnin inda Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da Dandalin Eagle da Majalisun Dokoki suke.

A Lagos, babban birnin kasuwanci na ƙasar, masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna a yankin Ikeja inda suka nufi gidan gwamnati domin bayyana rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwar da ake ciki.

A Kano, dandazon mutane sun hau kan tituna suna zanga-zanga inda suka riƙa kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan kawo sauƙi ga rayuwarsu.

Sai dai daga bisani zanga-zangar ta rikiɗe zuwa fashe-fashe da satar kayayyaki inda masu zanga-zangar suka kai hari kan wurare daban-daban, ciki har da cibiyar horarwa kan fasahar zamani ta gwamnatin tarayya wadda ake shirin ƙaddamarwa nan ba da jimawa ba.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun wawashe kayan da ke cikin cibiyar, ko da yake wasu bayanai na cewa 'yan sandan sun harbe wasu daga cikinsu.

A jihar Borno, gwamnati ta sanya dokar hana fita ta awa 24 a faɗin domin hana zanga-zangar rikiɗewa zuwa tarzoma.

Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Nahum Kenneth ya fitar ranar Alhamis ta ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da doka da oda sakamakon zanga-zangar da ke faruwa a faɗin Nijeriya kan tsadar rayuwa.

An jibje jami'an tsaro a birane daban-daban domin sanya ido da tabbatar da ganin an gudanar da zanga-zangar cikin oda.

Masu zanga-zanga suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu kamar "A kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya", "A dawo da tallafin man fetur" da sauransu./Hoto:Reuters
TRT Afrika