Hukumar hasashen yanayi ta Ghana (GMA) ta fitar da wata sanarwa ta gargadi a ranar Laraba, kan hazo da tsawa da guguwa da kuma ruwan sama wadanda ta yi hasashen 'yan ƙasar mazauna yankuna masu tsauni da dazuzzuka za su fuskanta, tana mai cewa akwai yiwuwar yanayin ''ya janyo duhu.''
Sanarwar na zuwa ne makonni biyu kacal bayan iftila'in ambaliyar ruwan sama a babban birnin ƙasar, lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa.
Hukumar GMA ta yi gargadin cewa ''guguwar da ta yi hasashe a kai cikin sanarwar gargadin da ta fitar tuni ta soma haifar da tsawa da ruwan sama a wasu yankunan gabas da arewacin ƙasar.''
''Tun daga sanyin safiya za a samo samu hazo da guguwar wadanda za su taso daga tsaunuka da kuma dazuzzuka, yanayin da ka iya janyo rashin gani,'' in ji sanarwar hasashen GMA.
Ƙasar wacce ke yankin yammacin Afirka ta yi ta fama da ruwan sama mai ƙarfin gaske a 'yan makonnin da suka gabata, inda hukumomi a makwabciyar ƙasar Nijeriya suka gargadi gwamnonin jihohi 31 da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
A shekarar 2021, mutum 150 ne suka mutu a wata gobara da ta tashi a wani gidan man fetur a birnin Accra, yayin da suke neman mafaka bayan da ruwan sama mai karfi da ambaliyar suka raba su da matsugunansu.