Shi ma Firaminista Shehbaz Sharif ya bayyana alhininsa game da mutuwar. / Hoto: AP Archive

Fiye da 'yan Pakistan 40 ne ake fargabar sun nutse a kifewar wani kwale-kwale a gabar tekun Atlantika na Yammacin Afirka, wanda ya zama babban wurin tashin 'yan gudun hijirar da ke son isa Turai.

Shugaba Asif Ali Zardari ya bayyana alhininsa game da mutuwar, ya kuma jaddada bukatar daukar tsauraran matakai don dakile safarar mutane.

Zardari ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Alhamis bayan wata kungiyar kare hakkin bakin haure da ke zaune a Spain, Walking Borders, ta ce mutane 50 ne suka mutu a kan hanyarsu ta zuwa Tsibirin Canary kuma 44 daga cikinsu 'yan Pakistan ne.

Kungiyar ta ce bakin hauren sun fara tafiyar ne a ranar 2 ga watan Janairu.

Shi ma Firaminista Shehbaz Sharif ya bayyana alhininsa game da mutuwar.

Pakistan ta ce ofishin jakadancinta da ke Morocco ya sanar da cewa wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 80 da suka hada da wasu 'yan Pakistan ya taso ne daga kasar Mauritania ya kife a kusa da Dakhla, wata tashar tashar jiragen ruwa da Moroko ke iko da ita a yankin Yammacin Sahara da ake takaddama a kai.

Kusan dukkan 'yan Pakistan da ke cikin jirgin sun fito ne daga garuruwan lardin Punjab da ke gabashin kasar.

'Yan'uwa sun taru a gidajen wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da wasu daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu ke tuntubar iyalansu a yanzu, kamar yadda jami'ai suka ce.

A Daska, wani birni a Punjab, dangin wasu mutane biyu sun ce dole ce ta saka su sayar da kadarori don tara miliyoyin kuɗi don biyan masu fataucin mutane don aika Arslan Ahmed da Mohammad Arfan zuwa Turai don neman ayyuka masu kyau.

Mahaifiyar Ahmed ta ce duk da ta ji ta bakin ‘yan'uwan ​​wasu da suka tsira cewa danta na raye amma har yanzu ba ta iya tuntubar shi ba.

Razia Bibi, mahaifiyar Arfan, ta bukaci hukumomi su nemo danta su dawo da shi.

Mafi muni a duniya

Miliyoyin mutane suna ƙaura zuwa Turai kowace shekara, mafi yawansu suna bin hanyoyin doka da wadanda aka saba da su.

Kasa da mutum 240,000 ne suka tsallaka kan iyakoki zuwa nahiyar ba tare da takarda ba a bara, a cewar hukumar kula da iyakokin Tarayyar Turai Frontex.

Yayin da hukumomi suka yi aiki don hana ƙaura da fasa kwauri daga ƙasashen da ke cikin Tekun Bahar Rum, ana ƙara yin amfani da hanyoyi masu haɗari.

Kamfanin Frontex ya ba da rahoton cewa sama da bakin haure 50,000 ne suka yi balaguro daga arewa maso yammacin Afirka zuwa Tsibirin Canary na Spain a cikin 2024, ciki har da 'yan Pakistan 178.

Kungiyar Walking Borders ta ce a cikin wani rahoto da ta fitar a makon da ya gabata, mutane 9,757 ne suka mutu ko kuma suka bace a kokarin tsallakawa zuwa tsibiran, inda ta kira hanyar "mafi kisa a duniya."

Tsibirin na da nisan kilomita 105 daga mafi kusa a Afirka, amma don guje wa jami'an tsaro, yawancin masu neman mafaka suna ƙoƙarin yin doguwar tafiya da za su ɗauki kwanaki ko makonni.

A bara, yawancinsu sun tashi daga Mauritania, wanda ke da akalla kilomita 762 daga tsibirin Canary mafi kusa, El Hierro.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce da dama da suka tsira da suka hada da 'yan Pakistan na zaune a wani sansani kusa da Dakhla.

Ofishin jakadancin Pakistan a Morocco yana tuntuɓar hukumomin yankin kuma jami'ai sun je Dakhla don taimakawa waɗanda suka tsira, a cewar sanarwar ma'aikatar.

Ma'aikatar ba ta bayyana adadin 'yan Pakistan da suka mutu ba. Jami’ai a ma’aikatar ba su kai ga samun karin bayani ba ranar Juma’a.

TRT World