Kwale-kwale uku dauke da sama da ‘yan ci-rani 300 ya bace a Tekun Atlantika, kamar yadda wata jami’a da ke aiki da hukumar bayar da agaji ga ‘yan ci-rani ta Walking Borders ta tabbatar a ranar Lahadi.
Helena Maleno, mai magana da yawun kungiyar, ta bayyana cewa kwale-kwalen sun bar Senegal kwanaki 15 da suka gabata zuwa Tsibirin Canary na Sifaniya.
Maleno ta bayyana cewa akwai ‘yan ci-rani wadanda ba su da takardu kusan 200 a cikin kwale-kwale daya, sai kuma kusan 65 a cikin kwale-kwalen na biyu da kuma na ukun mai dauke da mutum 60, wadanda suka soma tafiya daga kauyen Kafountine na kudancin Senegal.
Ta bayyana cewa iyalen ‘yan ci-ranin sun shiga damuwa sakamakon halin da suke ciki.
Munanan hanyoyi
Duk da cewa tsallaka teku domin ci-rani ba bisa ka’ida ba a tekun Afirka zuwa Tsibirin Canary na Sifaniya na daya daga cikin hanyoyin da ake bi a ‘yan shekarun nan, sai dai an gano cewa adadin yadda ake bin hanyar ya karu matuka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.
Akalla ‘yan ci-rani 559 suka rasu a yunkurinsu na zuwa tsibirin na Canary a 2022, daga ciki har da yara 22, kamar yadda bayanai daga Hukumar ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Kungiyar Walking Borders ta bayyana cewa adadin ‘yan gudun hijirar da suka rasa rayukansu a hanyar ya kai 1,784. Wannan na zuwa ne makonni bayan wani jirgin ruwa ya nutse a kusa da Tekun Greece a Bahar Rum inda mutum 80 suka rasu daruruwa kuma suka bace.