Daga Abdulwasiu Hassan
Moustafa Abdoulmoumini dan kasar Nijar ne da ke yawan tafiya zuwa Nouakchott babban birnin kasar Mauritaniya domin kasuwanci, inda yake yawan bin titi.
Yana shafe kwanaki biyu a hanya inda yake tafiyar kimanin kilomita 2,680 kafin ya kai inda zai je.
Duk da cewa duka kasashen suna Yammacin Afirka, zuwa Nouakchott daga Nijar aiki ne ja ga duk wanda zai yi tafiyar musamman idan ya yi kasafin kudi.
Rikicin da ake yi a Burkina Faso da Mali, inda ta nan ne hanyar da ta fi sauri, na nufin tafiya a mota na da hatsari kuma ba a cika so ba, duk da cewa ba lallai ita ce kadai mafita ba.
Tafiya da jirgi ma ba lamari ba ne mai sauki. Kamar akasarin kasashe da ke yankin, babu jirgi kai-tsaye daga kasashen biyu da ke Yammacin Afirka.
Tafiya a jirgi daga Mauritania zuwa Yamai na daukar kusan awa hudu.
Hakan ya sa Moustafa da duk wani da ke tafiya tsakanin Mauritania zuwa Nijar ba tare da jirgi ba ya zama ba shi da zabi.
Hakan ya sa mutane na kasadar bin mota ta cikin Burkina Faso da Mali, ko kuma su biya karin kudi domin shiga jirgi da kuma kara shafe wasu sa’o’i suna jira a wurin yada zango kafin kuma su sake shiga mota.
Jinkiri a tafiya da jirgin sama
Moustafa na sane da cewa idan ya hau jirgi daga Nouakchott zuwa Yamai da ke Nijar, zai shafe sa’o’i da dama a wata kasa kafin ya ci gaba da tafiya.
Ga wani wanda ya san cewa tafiyarsa za ta samu cikas sakamakon jinkiri mai tsawo, wani lokaci ma tsawon kwana guda, mutum za a iya biyansa kudinsa sakamakon jinkirin.
“Kada ka razana idan ka isa filin jirgi aka shaida maka cewa an soke jirgin da za ka shiga,” in ji tsohon ministan Nijar, Mahaman Laouan Gaya, wanda yana yawan sufuri da jirgin sama a Yammacin Afirka.
“Hakan ya faru da ni sau uku. A Lome (Togo) da muka yada zango, sai aka sanar da mu cewa babu jirgin da zai yi jigilar mu zuwa inda za mu!” in ji shi.
Rashin samun jirgin da zai kai ka wuri kai tsaye da jirgin yawo na sa tafiya a tsakanin Yammacin Afirka ta kasance da wahala.
“Za a iya tafiya da cewa karancin jiragen haya na kara kudin tikitin jirgi. Wuraren da ake yawan samun tashin jirage sun hada da (Arewacin Afirka da Kudancin Afirka, da wasu wurare da ke wajen Afirka),” kamar yadda Gaya ya shaida wa TRT Afrika.
Ba wai matsalar tafiya mai tsawo da kuma lokaci mai tsawo da ake shafewa a filin jirgi kadai ba, wannan matsalar tana hana mutane da dama fitar kasashensu domin neman damar kasuwanci a Yammacin Afirka.
Kalubalen kan titi
Bin titi shi ne mafita ga wadanda ba su son su fuskanci bacin rai sakamakon jinkirin jiragen sama.
Duk da cewa daya daga cikin muradan kungiyar Ecowas shi ne jama’ar yankin na Yammacin Afirka su iya walwala a yankin ba tare da shinge ba, masana sun ce wani tsari wanda masu mulkin mallaka suka bari, da kuma matsaloli da suka shafi gudanarwa da tsaro na kawo cikas ga walwalar jama’a.
“A lokacin da muka zo nan a karon farko, mun shafe kwanaki 13 a kan hanya,” in ji Yusuf Mohammed, wani dan Nijeriya da ke yin kasuwancinsa a Nouakchott, kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Za zarar ka bar Nijeriya da Nijar, tafiyar tana kara wahala.” Yusuf na zargin cewa a wani lokaci jami’ai a kan hanya na karbar kudi daga fasinjoji, inda a wani lokaci suke bayar da kudin da ya zarta kudin motarsu ma.
“A duk wani shingen bincike, sai ka biya kudi,” in ji shi. “Wasu ma sai su zarge ka da saba doka sakamakon wasu daga cikin takardunka inda za su bukaci ka biya,” kamar yadda ya kara da cewa.
Idan mutum ya kammala da jami’ain kula da shige da fice da kuma na kwastam a kan iyaka, mutum zai fi walwala cikin sauki ba tare da an tambaye shi cin hanci ba.
Wahala biyu
Masana sun bayyana cewa matsalolin da jama’ar Yammacin Afrika ke fuskanta yayin da suke tafiya da mota a yankin sun wuce tunani.
“Wahalhalun da ake fuskanta a kan titi sun dunkule sun koma kalubalen tafiya da jirigi. Mutane ba su kuma son zuwa wadannan kasashen, sakamakon wahalar da suka sha a hanya,” kamar yadda masanin sufurin jirgin sama Olumide Ohunayo ya shaida wa TRT Afirka.
Wannan matsala ta samo asali ne sakamakon karancin jiragen sama da mutum miliyan 430 da ke Yammacin Afirka ke fuskanta.
Duk da cewa wani rahoto na Bankin Duniya ya bayyana cewa cikin kashi 100 na sufurin jirgin sama Afirka ce ke da kashi daya, masana na ganin samun jirgin yawo ya fi rauni a Yammacin Afirka fiye da Arewaci ko kuma Kudancin nahiyar.
Haka kuma raunin da ke da akwai na tituna da kuma tafiyar jirgin sama tsakanin yankin yana kawo cikas ga mu’amula da ake yi tsakanin jama’ar Yammacin Afirka da kuma damar da suke da ita ta yin kasuwanci tattare.
Mafita
Idan aka ci gaba da samun matsalar sufuri tsakanin kasashen Yammacin Afirka, hakan zai kawo cikas wurin cimma burin hade kan yankin ba tare da shinge ba da kuma kara inganta rayuwar mazauna Yammacin Afirka.
Masana na ganin akwai bukatar gwamnatocin kasashen Yammacin Afirka su mayar da hankali wurin kula da bukatun kungiyar Ecowas.
“Ya kamata mu san cewa duka yarjejeniyar da muka saka wa hannu a matsayinmu na mambobin Ecowas su wuce batun takarda. Ya kamata a aiwatar da su, ta yadda mutane za su iya barin kasashensu da ke yankunansu da kuma zuwa wata kasa ba tare da wata wahala ba,” in ji Olumide.
Wata matsala kuma da masana suka ce ya kamata a duba shi ne na haraji mai yawa, wanda aka saka shi domin kare jiragen cikin gida daga jirage na kasashen waje masu gasa.
Harajin da ake saka wa jiragen sama yana dawowa ne kan fasinjoji, wanda hakan yake sa jiragen su kara tsada fiye da kima.
Masu kananan sana'o'i kamar Moustafa da Yusuf na burin ganin ranar da za su iya yawo tsakanin kasashen Afirka ba tare da wahala ba.
Suna ganin hakan ba wai zai kawo musu sauki kawai a rayuwa ba, zai amfani tattalin arzikin yankin.