Fiye da matasa ‘yan bindiga 500 da ke cikin ƙungiyoyin ‘yan tawaye da na ‘yan ta’adda ne suka ajiye makamansu sakamakon kiran da shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya yi game da rungumar zaman lafiya.
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa Ministan Cikin Gida da Tsaron Al’umma na ƙasar, Janar Mohamed Toumba, ne ya faɗi hakan a birin Yamai a ƙarshen mako.
Kamfanin ya ambato ministan yana cewa an raba waɗanda suka ajiye makamansu cikin sansanoni biyu.
Ya ce sansanonin biyu su ne, sansanin Hamdalaye da ke jihar Tillaeri da kuma sansanin Goudoumari da ke jihar Diffa.
“Tattabar da zaman lafiya na buƙatar haɗin-kai da kuma zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban,” in ji ministan, yana mai ƙarawa da cewa gwamnati ta “ɗauki matakai daban-daban ta hanyar kwamitoci na ƙananan hukumomi domin wayar da kan jama’a.”
Kazalika kamfanin labarai na ANP ya ambato Janar Toumba yana cewa “Muna kuma ƙoƙarin isar da saƙon shugaban ƙasa ga waɗannan matasan da suka samu kansu cikin ƙungiyoyin su koma ga ƙasarsu domin mu gina Nijar saboda jin daɗinmu.”
Ya ƙara da cewa gwamnatinsu ta mayar da hankali ne kan gina hanyoyi domin inganta haɗin-kan ƙasar.
Ƙungiyo masu zama da kansu
Har ila yau, ministan ya ce ƙasar tana sa ido kan ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu a ƙasar ne domin da yawa daga cikinsu ba su da rajistar aiki a Jamhuriyar Nijar.
"Mun yi mamakin ganin cewa mun ƙirga sanannun ƙungiyoyi masu zaman kansu har guda 4,122 ciki har da 332 na ƙasashen waje," in ji ministan yana mai cewa yana ganin cewa waɗannan ƙungiyoyin masu zama da kansu a matsayin wani ɓangare da mutane suke zama ba tare da yi wa ƙasarsu aiki ba.
Ya ƙara da cewa ƙungiyoyin sun yi iƙirarin kashe biliyan 130, kuɗin da ba za a iya tabbatar da an kashe ba.
“Ina cikin waɗanda suke da tabbacin cewa ƙungiyoyi masu zaman kansu ba su taɓa gina wata ƙasa ba, tallafi bai taɓa gina wata ƙasa ba,” yana mai cewa “idan muna son mu ci gaba dole mu ci gaba ta hanyar da ta dace, ta hanyar dogaro da kanmu."
Ya ce bincike ya nuna cewa wasu daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu suna haɗa baki da ƙasashen da ke yaƙar Nijar.
Wannan shi ya sa Nijar to kori wasu daga cikin ƙungiyion kuma take tabbatar da cewa tana da iko kan duk inda sauran ƙungiyoyin za su je a faɗin ƙasar, in ji Janar Toumba.